Sheikh Gumi ya bayyana dalilinsa na shiga daji yin wa'azi

Sheikh Gumi ya bayyana dalilinsa na shiga daji yin wa'azi

- Babban Malami Sheikh Ahmad Gumi ya sanar da dalilinsa na shiga daji wa'azi

- Ya ce yin hakan yana da alaka da lamarin garkuwa da mutane da yayi yawa a kasar nan

- A cewarsa, akwai bukatar a koyar da su addini domin su gane abinda suke ba addini bane

Kamar yadda BBC Hausa ta yi hira da babban malami, Sheikh Gumi a kan dalilinsa na shiga yankuna masu tsananin hadari domin da'awa, malamin ya bayyana dalilinsa.

Malamin ya bayyana dalilansa biyu na yin hakan. Ya ce: "Wadannan bayin Allah dai makiyaya ne kuma a daji suke zama. Suna matukar bukatar wanda zai koyar musu da addini. Akwai bukatar su fita daga cikin jahilcin da suka tsinci kansu. Bautar Allah ta zama dole."

Malamin ya tabbatar da cewa barnar da suka fada ta samo asali ne da rashin ilimin da suke ciki.

KU KARANTA: Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

Sheikh Gumi ya bayyana dalilinsa na shiga daji yin wa'azi
Sheikh Gumi ya bayyana dalilinsa na shiga daji yin wa'azi. Hoto daga BBCHausa
Source: Twitter

"Mutumin da ya fada halin fyade, shaye-shaye da kwace dukiyar jama'a, ya za a yi ya gane cewa abinda yake ba kyau? Dole sai da saitin addini. To kuma babu shi.

"Matukar aka koya musu addini, hakan zai basu kariya daga barnar da suke aikatawa," cewar babban malamin.

Malamin ya tabbatar da cewa masu wadannan sace-sacen suna da iyayen gida saboda sau da yawa masu satar ba wani abu mai yawa ake biyansu ba bayan sun karba kudin fansar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa

A wani labari na daban, mazauna karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro bayan sace 'yan mata uku da mayakan Boko Haram suka yi.

Madagali tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da mayakan Boko Haram suka kwace a 2014 kafin sojin Najeriya su kwato su a 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan mata biyu tare da matar aure daya ne ke aiki a gona a makon da ya gabata a wani kauyen Dar yayin da wasu mutane dauke da makamai suka cafkesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel