Gwamna Kebbi Bagudu ya ware N464m don tallafawa mata a jihar

Gwamna Kebbi Bagudu ya ware N464m don tallafawa mata a jihar

- Gwamnan jihar Kebbi ya ware makudan kudade don tallafawa mata a wasu kananan hukumomi

- Gwamnan zai bada kudaden ta ma'aiktar harkokin mata da ci gaban al'umma

- A baya dama gwamnan ya fara tallafawa matan a fannin noman tumatir

Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya amince da cire Naira miliyan 468.5 don aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen karfafa gwiwa a karkashin Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci Gaban Jama’a.

Aisha Maikurata, babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma, ta bayyana haka lokacin da take zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.

ya ce: “A wani bangare na ci gaba da kokarin da Gwamna Atiku Bagudu ke yi na rage talauci da daukaka darajar rayuwar jama’a, musamman ma marasa karfi a jihar, gwamnan ya amince da aiwatar da ayyukan da suka kai na Naira miliyan 468.5 ga ma’aikatar.

KU KARANTA: Wata kungiya ta nemi Amaechi ya yi murabus kan batun tashar Baro

Gwamna Kebbi Bagudu ya ware N464m don tallafawa mata a jihar
Gwamna Kebbi Bagudu ya ware N464m don tallafawa mata a jihar Hoto: The Guardian
Asali: UGC

“Ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma za ta shiga a dama da ita wajen aiwatar da ayyukan a mahimman wurare a cikin ƙananan hukumomi 11 da Majalisar Dokokin jihar Kebbi ta gano.”

A cewar ta, kananan hukumomin da aka ware don ayyukan sun hada da, Gwandu, Koko / Besse, Aliero, Maiyama, Jega, Bagudu, Fakai, Ngaski, Argungu, Danko / Wasagu da Yauri.

Ta bayyana cewa makasudin ayyukan shi ne karfafawa manoma, zawarawa, marayu da matasa gami da mata masu rauni masu shiga cikin harkokin tattalin arziki a kananan hukumomin.

"Kudin da ma'aikatar za ta kashe kan aiwatar da ayyukan na daga cikin Naira biliyan biyu da gwamnan ya saki don ayyukan mazabu a duk fadin jihar," inji ta.

Misis Maikurata ta kuma ce kwanan nan gwamnatin ta samar da tallafi ga mata 350 a harkar kasuwancin tumatir a fadin jihar don karfafa tattalin arzikin.

"Wannan yana daga cikin wasu shirye-shiryen karfafa tattalin arziki daban-daban da aka fara a jihar inda suka samu N30,000 kowanne," inji ta.

Sakataren din-din-din ya yaba da irin goyon bayan da gwamnan ke baiwa ma'aikatar tare da nuna damuwa da kauna ga marayu da kuma marasa karfi a jihar.

KU KARANTA: Babban hadari ne gwamnati ta ci bashin N9.8tn - Fitch Ratings

A wani labarin, Masu cin gajiyar N-Power, wadanda suka kammala shirin aikin na shekaru biyu, yanzu za su sami damar samun aikin dindindin ko damar kasuwanci, in ji Gwamnatin Tarayya.

Wannan wani bangare ne na sabuwar kokarin gwamnati kan fita daga tsarin N-power.

Tsarin an yi shine ga dukkan 'yan tsarin A da B na shirin N-Power.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel