Raba ni! Maganar da ake yi cewa zan shiga APC ba gaskiya ba ne inji Ikpeazu

Raba ni! Maganar da ake yi cewa zan shiga APC ba gaskiya ba ne inji Ikpeazu

- Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, ya ce bai da niyyar komawa jam’iyyar APC

- Okezie Ikpeazu ya ce Abia jihar PDP ce, don haka ba zai taba sauya-sheka ba

- Jagoran na jam’iyyar hamayyar ya ce PDP ce za ta sake karbe jiharsa a 2023

Gwamnan Abia, Okezie Victor Ikpeazu, ya karyata rahotannin da ke yawo na cewa wasu dinbin magoya bayan jam’iyyar PDP za su sauya-sheka a jiharsa.

Ana ta rade-radin cewa gwamna da wasu ‘ya ‘yan PDP da-dama za su koma jam’iyyar APC a Abia.

Gwamna Okezie Victor Ikpeazu ya shaida wa ‘yan jam’iyyarsa cewa wannan magana da ke ta yawo ba gaskiya ba ce, ya ce su na nan daram-dam-dam a PDP.

Jaridar The Guardian ta rahoto Okezie Victor Ikpeazu ya na cewa zai mika mulki ne ga gwamnan PDP a 2023, lokacin da wa’adinsa na shekaru takwas zai kare.

KU KARANTA: Sule Lamido ya ragargaji Buhari, ya ce gwamnatinsa ta hada fada

Mai girma Victor Ikpeazu ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron PDP da aka yi a garin Umuahia, jihar Abia, gwamnan ya ce jam’iyyarsu ke da al’umma.

Victor Ikpeazu ya fada wa ‘ya ‘yan PDP ka da su damu da abin da ya faru da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka tsere saboda kin yi masu alkawarin tikitin 2023.

A wannan taro wanda shi ne na farko da PDP ta yi a shekarar nan a Abia, gwamnan ya ce dole a taru a hada-kai, domin cin ribar gumin da jam’iyyar ta ci a hanya.

“PDP ta na nan da karfinta da aka sani a jihar nan. Rade-radin cewa ina shirin sauya-sheka bai da asali.”

KU KARANTA: Kungiyar Magoya bayan Tinubu ta na kai wa Sarakuna ziyara

Raba ni! Maganar da ake yi cewa zan shiga APC ba gaskiya ba ne inji Ikpeazu
Gwamna Okezie Ikpeazu Hoto: www.thisdaylive.com
Source: UGC

“Babu dalilin tada hankali a dalilin rade-radin sauya-shekar wasu ‘ya ‘yan PDP zuwa wasu jam’iyyun.” Inji Ikpeazu ya na mai kiran a ajiye son-kai, ayi aiki.

Da alamu gwamnan jihar Oyo, ya dauki bangaraen Fulani, ya ce ka da a hana mutane kiwo. Hakan na zuwa ne bayan gwamnan Ondo ya ce Makiyaya su bar jeji.

Gwamna Seyi Makinde ya na da ra'ayin cewa ba daidai ba ne wani ya fito ya ba Makiyaya Fulani wa’adi su bar daji inda su ke neman abincin da za su ba dabbobinsu.

Makinde ya ce ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ne abokan fada ba Makiyaya ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel