Tsohon Gwamnan Jigawa ya zargi Gwamnatin APC da jawo rashin hadin-kai a kasa
- Sule Lamido ya zargi Gwamnatin APC mai-ci da jawo rabuwar kan jama’a
- Tsohon Gwamnan ya ce matsalolin da ake fama da su a yau sun zarce na da
- Sule na cikin rikakkun ‘yan adawa na Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki gwamnatin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta a Najeriya tun 2015.
Jaridar Vanguard ta rahoto gawurataccen ‘dan adawar ya na zargin gwamnatin Muhammadu Buhari da kawo rashin hadin-kai tsakanin al’umma.
Sule Lamido ya nuna hakan ne a lokacin da yake jawabi a ranar Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, wajen rantsar da kwamitin sasancin PDP a Jigawa.
Alhaji Sule Lamido ya ce kafin jam’iyyar APC ta karbi mulki, ta rika zargin gwamnatin PDP da hannu a rikicin Boko Haram da duk wasu zargin sata.
KU KARANTA: Tsohon Jami’in Gwamnati ya tona wa Ministan Jonathan asiri a kotu
Sule ya ce duk da zargin rashin gaskiyar da aka yi masu, abubuwa ba su gyaru ba a hannun APC.
A cewar ‘dan siyasar, bayan jam’iyyarsu ta PDP ta rasa mulki, matsalolin da aka yi fama da su a da, sun kara tabarbarewa a karkashin gwamnati mai-ci.
“Ko da sun zarge mu da Boko Haram, yau ana fama da rikicin ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a mulkinsu, babu alamun za a kawo karshen matsalar.”
Ya ce: “Ana yanka mutane, ana kashesu a gidajensu, garuruwansu, ana tada kauyuka gaba daya, yayin da ake wulakanta mata a gaban idan masu mulki yau.”
KU KARANA: Rashin tsaro ya jawowa Buhari bakin jini a Arewa - Bafarawa
Tsohon gwamnan ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsu ta PDP su bada hadin-kai, ya ce kwamitin da aka rantsar zai yi kokarin sulhu ne a reshen jam’iyyar.
A na sa bangare, shugaban PDP na jihar Jigawa, Babandi Ibrahim, yace jam’iyya za ta yi kokarin ganin ta shawo kan wadanda aka yi wa ba daidai ba.
A jiyan ne kuma aka ji Alhaji Sule Lamido, ya na magana game zaben 2023 da 'dan siyasar nan da ake sa ran zai yi takara a jam'iyyar APC, Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya rantse cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba mara wa takarar Bola Tinubu baya idan 2023 ta zo ba.
Sule Lamido ya kuma kalubalanci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya nuna mutanen da yake ikirarin sun fitar da su daga cikin talauci a Jigawa
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng