Wata kungiya ta nemi Amaechi ya yi murabus kan batun tashar Baro

Wata kungiya ta nemi Amaechi ya yi murabus kan batun tashar Baro

- Wata kungiya ya nemi Rotimi Amaechi da ya yi murabus a kan kujerarsa ta minista

- Kungiyar ta bayyana cewa Amaechi ya karfafa barnatar da kudade kan ayyukan da ba za su amfani kasa ba

- Amaechi ya bayyana cewa aikinsa a matsayin minista na gina tashar Baro ya kammala

Wata kungiya mai suna, ‘Maritime Industry Advocacy Initiative’, ta yi kira ga Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da ya sauka daga mukaminsa saboda kalaman da ya yi kan tashoshin jiragen ruwa guda hudu, wadanda ke jihohin Anambra, Imo, Kogi da Neja.

Ministan ya yi wata tattaunawa da Hukumar Talabijin ta Najeriya inda ya bayyana gina tashoshin jiragen ruwa a duk fadin kasar a matsayin barnatar da dukiyar al’umma, yana mai jaddada cewa ba su ne ayyukan da za a yi amfani da su ba.

Ya ce idan ba a tono Kogin Niger ba, babu jirgin ruwan da zai iya zuwa tashar Baro.

KU KARANTA: Malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6

Wata kungiya ta nemi Amaechi ya yi murabus kan batun tashar Baro
Wata kungiya ta nemi Amaechi ya yi murabus kan batun tashar Baro Hoto: Gambeta News
Asali: UGC

An ruwaito shi yana cewa: “Sun so a gina tashar; don haka muka kammala shi. Hakkina shine in gina tashar Baro kuma na gina ta. A matsayina na Minista, na jawo hankalin jama’a cewa wadannan su ne matsalolin da za mu fuskanta idan muka gama wannan tashar ta Baro.

“Na farko Nijeriya ba ta samar da komai tun farko; don haka me za ku safara? Idan muka sa tashar jirgin ruwan Apapa ya zama mai inganci, to ba mu ma da isassun kaya."

Wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Daraktan kamfanin MAIN, Sesan Onileimo, kuma aka aike wa wakilin The Punch ta bukaci ministan da ya yi murabus saboda barnatar da kudaden shiga a kan aikin da ya san ba zai yiwu ba.

Wani bangare na sanarwar ya karanta, “Muna kira ga Ministan Sufuri, Mista Rotimi Amaechi, da ya yi murabus saboda karfafa barnatar kudaden shiga a tashoshin jiragen ruwan kasar nan.

KU KARANTA: Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje

A wani labarin, Rukunin kamfanonin Dangote ya kammala shimfida mafi tsawon titin kankare a Najeriya a jihar Kogi. Ita ce irinta ta farko, a cewar manyan injiniyoyi, Reuben Abati ya ruwaito.

Masu motoci sun bayyana hanyar Obajana-Kabba mai tsawon kilomita 43, wanda kamfanin Dangote Industries Limited (DIL) ya gina, a matsayin babbar hanyar kasar da ta fi dacewa wajen taimaka wa matafiya tsakanin Arewa da Kudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel