Babban hadari ne gwamnati ta ci bashin N9.8tn - Fitch Ratings

Babban hadari ne gwamnati ta ci bashin N9.8tn - Fitch Ratings

- Wani babban kamfani mai suna Fitch Ratings ya bayyana hadarin da ke cikin ci gaba da cin bashin da Najeriya ke yi

- Kamfanin ya siffanta ci gaba da cin bashin zai iya raunata tattalin arzikin kasar

- Kamfanin ya fidda alkaluman yadda bashin yake illata tattalin arzikin a hankali

Fitch Ratings ta bayanna cewa akwai hadari sosai yadda gwamnatin tarayya ke cin bashi don cimma burin kasafin kudin kasar. Fitch ta nuna hakan na iya raunata tattalin arzikin kasar.

Fitch Ratings ta bayyana hakan ne a cikin rahoton ta na ranar Laraba mai taken ‘Nigeria’s deficit monetisation may raise macro-stability risks’, The Punch ta ruwaito.

Wani sashi na rahoton ya karanta, “Tsayayyiyan amfani da kudaden kai tsaye na iya haifar da hadari ga daidaituwar tattalin arziki - idan aka yi la’akari da raunin tsare-tsaren hukumomi a yanzu - amma muna sa ran FGN za ta rage kashe kudadenta a 2021.

KU KARANTA: Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje

Babban hadari ne gwamnati ta ci bashin N9.8tn - Fitch Ratings
Babban hadari ne gwamnati ta ci bashin N9.8tn - Fitch Ratings Hurriyet Daily News
Source: UGC

“FGN kai tsaye ta ci bashin 1.9% na GDP daga CBN don daukar nauyin gibin kasafin kudinta a shekarar 2020, wanda Fitch ya kiyasta a 3.6% na Gross Jimillar Arzikin Cikin Gida.

“Kasuwanni da dama da suka kunno kai sun yi amfani da kudaden gibin babban banki a shekarar 2020 bisa la’akari da bukatun kashe kudade cikin gaggawa da kuma wargajewar kasauwanni na wucin gadi hade da cutar coronavirus.

"Duk da haka, amfani da kudin babban banki a Najeriya ya riga ya faru dalilin mummunar annoba."

Rahoton ya kara da cewa, “Mun kiyasta cewa adadin WMF na gwamnati da CBN ya kai kimanin naira tiriliyan 9.8 (kwatankwacin 6.7% na GDP) a karshen shekarar 2019, daga N5.4tn (4.2% na GDP) a karshen 2018.

“Ba kamar gwamnati ba, mun sanya wannan ma'auni a ma'auninmu na bashin gwamnatin Najeriya. Cin bashi daga cibiyar ya kai 30% na bashin FGN a karshen shekarar 2019, a kiyasin mu."

KU KARANTA: Malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6

A wani labarin, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo (SAN) ya ce hangen nesan gwamnatin Buhari na fitar da akalla ‘yan Najeriya miliyan 20 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu masu zuwa yanzu ya kusa.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 19 ga watan Janairu a Abuja yayin fara shirin fara hada hadar kudade da gwamnatin tarayya ta fara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel