Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje

Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'azziyarsa ga iyalan tsohon ministan wasanni na kasa

- Shugaban ya bayyana cewa mamacin ya kasance mutumin kirki kuma mai aiki tukuru a fanninsa

- Buhari ya masa addu'ar Allah ya kyautata makwancinsa da kuma bai wa na kusa dashi hakurin jure rashinsa

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a ranar Laraba, ya yi jimamin tsohon Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni, Bala Ka’oje, wanda ya mutu kwanan nan.

Sakon ta’aziyyar ta Buhari ga dangin mamacin da sauran mutane na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu, mai taken “Shugaba Buhari na jimamin tsohon Ministan Wasanni, Ka’oje.”

Sanarwar ta karanta, “Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika ta’aziyya ga iyalen Ka’oje, gwamnati da al’ummar jihar Kebbi bisa rasuwar Hon. Bala Bawa Ka’oje, tsohon Ministan Matasa da ci gaban wasanni.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Kotu ta bayar da belin Sowore a kan kudi Naira miliyan 20

Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje
Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje Hoto: Daily Post
Source: UGC

“Shugaba Buhari ya lura cewa a matsayinsa na tsohon dan majalisar wakilai, shugaban al’umma kuma jigo a jam’iyyar APC.

"Hon. Ka'oje ya yi imani kwarai da gaske wajen yi wa mutane hidima tare da sadaukarwa kuma za a yi kewarsa sosai saboda soyayyarsa ga wasu.

"Shugaban kasar yana addu'ar samun hutu na rayuwar wanda ya mutu da kuma ta'aziyya ga dangi, abokai da abokan arziki."

KU KARANTA: Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo

A wani labarin, Bala Bawa Ka’oje tsohon Ministan Wasanni, ya mutu yana da shekaru 60.

A cikin wata sanarwa mai taken ‘Tsohon Ministan Wasanni Ka’oje ya mutu yana da shekara 60, aka binne shi a Abuja" a ranar Talata, kakakin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Ademola Olajire, ya ce ’yan uwa a fannin wasanni a kasar sun shiga cikin jimami da mutuwar Ka’oje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel