Hadari a hanyar Abuja zuwa Lokoja ya kashe mutum 3, 13 sun jikkata

Hadari a hanyar Abuja zuwa Lokoja ya kashe mutum 3, 13 sun jikkata

- Hadarin mota ya rutsa da wasu mutane 3 a hanyar Abuja zuwa Lokoja

- Hadarin yayi sanadiyyar mutuwar wasu yayin da mutum 13 suka jikkata

- Rahoto ya bayyana lambobin motocin da hadarin ya rufta dasu

Mutum uku sun mutu a ranar Laraba yayin da wasu 13 suka samu raunuka a wani hatsarin mota a kauyen Gada-Biyu, kan hanyar Abuja zuwa Lokoja, Aminiya ta ruwaito.

Hatsarin ya rutsa da motar Toyota Corolla mai lamba KFU 160 AA da kuma motar Toyota Hiace mai lamba EBJ 422 XA.

An ga mazauna yankin suna kokarin ceto wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su yayin da suka makale cikin motocin wadanda suka afka cikin wata motar tipper da ke ajiye a gefen hanya.

KU KARANTA: Malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6

Hadarin mota a hanyar Abuja zuwa Lokoja ya kashe mutum 3, 13 sun jikkata
Hadarin mota a hanyar Abuja zuwa Lokoja ya kashe mutum 3, 13 sun jikkata Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Wani ganau ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 2:12 na rana “lokacin da bas din da ke dauke da man ja da fasinjojin da ke zuwa daga Lokoja suka kwace ta daki motar Corolla sai motocin biyu suka fada cikin wata motar tipper da ke ajiye a gefen hanya,” inji shi.

Lokacin da aka tuntubi kwamandan reshen Abaji na FRSC, ACC Abubakar Shehu Dogondaji, ya ce ba ya ofishinsa sai dai ya umarci mutanensa da su je wurin domin ceto bayan an kira shi a waya.

KU KARANTA: Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje

A wani labarin, Rukunin kamfanonin Dangote ya kammala shimfida mafi tsawon titin kankare a Najeriya a jihar Kogi. Ita ce irinta ta farko, a cewar manyan injiniyoyi, Reuben Abati ya ruwaito.

Masu motoci sun bayyana hanyar Obajana-Kabba mai tsawon kilomita 43, wanda kamfanin Dangote Industries Limited (DIL) ya gina, a matsayin babbar hanyar kasar da ta fi dacewa wajen taimaka wa matafiya tsakanin Arewa da Kudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.