Labari mai dadi: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG

Labari mai dadi: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG

- FG ta fito da tsare-tsare don fitar da yan Najeriya daga kangin talauci

- Hakan na zuwa ne a yayinda gwamnati ta sanar da shirin raba N5,000 ga yan Najeriya miliyan 24

- A cewar ministar walwala, Sadiya Farouq, za a dunga biyan kudin ne na tsawon watanni shida

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a ba yan Najeriya miliyan 24, kowannensu N5000 na tsawon watanni shida daga cikin kokarin gwamnati mai ci na fitar da mutane daga kangin talauci.

Ma’aikatar harkokin agaji da magance annoba ce ta bayyana hakan a ranar Talata, 19 ga watan Janairu.

Da take Karin haske a kan lamarin a Abuja ta wani jawabi daga hadimarta Nneka Anibeze, ministar walwala, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce shirin zai gano tare da yi wa mutanen da ba a yiwa rijista a baya ba rijista domin basu tallafin, jaridar Punch ta ruwaito.

Labari mai dadi: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG
Labari mai dadi: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG Hoto: @Sadiya_farouq
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: 2023: Daga karshe tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan batun dawowarsa kujerar

Mun jajirce don fitar da yan Najeriya daga kangin talauci – Buhari

Legit.ng ta tuna cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba da wasa gwamnatinsa ta ke yi a maganar maganin talauci ba.

Mai girma Muhammadu Buhari wanda ya ce babu gwamnatin da ta kawo tsare-tsare da za su taimaka wa matasa, ya inganta kokarin gwamnatinsa.

Shugaban kasar yayi magana ta dandalin sada zumunta na zamani na Twitter, yace an kara yawan mutanen da suke amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Dattijo mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a jiya ya ce majalisar tarayya bata da dalilin da zai sa ta yaki shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda tana son farantawa wasu rai a kasar nan.

Lawan ya sanar da hakan ne a yayin da ya karbar wakilai daga jihar Adamawa wadanda suka ziyarcesa domin nuna jin dadi ga majalisar tarayya a kan yadda ta sauya jami'ar Modibbo Adama da ke Yola.

Wakilan sun samu jagorancin Sanata Aishatu dahiru Ahmed da kuma shugaban jami'ar, farfesa Abdullahi Lima Tukur, Vanguard ta wallafa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng