Bayan shekara 1, an gaza gano iyayen yaran Gombe 18 da aka ceto, an mayar da su Anambara

Bayan shekara 1, an gaza gano iyayen yaran Gombe 18 da aka ceto, an mayar da su Anambara

- An sacesu a Gombe, an kai su Anambara, an cetosu an mayar da su Gombe, yanzu kuma an sake mayar da su Anambara

- Bayan sama da shekara daya da cetosu, ba'a samu iyayensu a Gombe

- An yanke shawaran mayar da su Anambara tun da lamarin ya kasance haka

Hukumar yan sanda ta bayyana cewa yara 18 da aka ceto daga hannun matar da ta sace su daga jihohin Arewa, har yanzu ba'a gano iyayensu ba bayan shekara guda.

Yaran yanzu haka suna hannun ma'aikatar harkokin mata da yara na jihar Anambara.

A wani jawabin da kakakin hukumar yan sandan jihar, CSP Haruna Mohammed, ya saki, ya bukaci duk wanda ke da masaniya game da iyayen yaran ya tuntubi Area Command Onitsha, 3-3 Divisional Police Station, Nkwelle Ezunaka, ko ya kira kakakin yan sandan Anambara a lambar waya 08060970639.

Za ku tuna cewa a ranar 20 ga Oktoba 2019, an ceto wasu yara da wata mata Hauwa Usman take sacewa tana kaiwa abokiyarta dake Anambra.

Bayan bincike, an damke mata 3 a karamar hukumar Idemili North na jihar Anambra da yara uku cikin wadanda aka sace.

"Bincike ya nuna cewa wata mata Hauwa Usman ta sace yaran a ranar 20/10/2019 kuma ta kaiwa abokan aikinta dake Anambra," Kakakin yan sandan Anambra, DSP Mohammed Haruna ya bayyana.

Yanzu hukumar yan sandan jihar Gombe ta mayar da yaran Anambra saboda har yanzu ba'a samu iyayensu ba.

Bayan shekara 1, an gaza gano iyayen yaran Gombe 18 da aka ceto, an mayar da su Anambara
Bayan shekara 1, an gaza gano iyayen yaran Gombe 18 da aka ceto, an mayar da su Anambara Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel