Buhari: Da gaske muke wajen ganin an ceto mutum miliyan 100 daga talauci a kasa

Buhari: Da gaske muke wajen ganin an ceto mutum miliyan 100 daga talauci a kasa

- Gwamnatin Tarayya ta ce maganar ceto mutane miliyan 100 daga talauci na nan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudirinsa a shafin Twitter a jiya

- An ribanya adadin wadanda zasu amfana da tsare-tsaren N-Power da kuma GEEP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba da wasa gwamnatinsa ta ke yi a maganar maganin talauci ba.

Mai girma Muhammadu Buhari wanda ya ce babu gwamnatin da ta kawo tsare-tsare da za su taimaka wa matasa, ya inganta kokarin gwamnatinsa.

Shugaban kasar yayi magana ta dandalin sada zumunta na zamani na Twitter, yace an kara yawan mutanen da suke amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa.

Buhari ya bayyana wannan ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, 2020 da karfe 4:09 na rana.

KU KARANTA: Watakila matsin tattalin arzikin Najeriya ya kai 2023

“Muna nan kan bakarmu na ceto mutanen Najeriya miliyan 100 daga talauci.” Inji shugaban kasar.

@MBuhari ya ce: “A game da wannan na kara adadin mutanen da ake amfana da tsare-tsaren inganta rayuwar marasa karfi.”

“Mun ribanya masu cin moriyar @npower_ng zuwa mutane miliyan daya, sababbin mutane miliyan daya da za su amfana da tsarin @geep_ng.”

Gwamnatin APC mai-ci ta shigo da tsarin GEEP watau 'Government Enterprise and Empowerment Programme’ ne domin tallafa wa masu karamin karfi.

KU KARANTA: Sarkin Ife ya bude gidauniyar da za ta rika tura Matasa zuwa jami’a

Buhari: Da gaske muke wajen ganin an ceto mutum miliyan 100 daga talauci a kasa
Shugaban Najeriya Buhari Hoto; vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban Najeriyar bai tsaya nan ba, ya ce an kara yara miliyan biyar cikin ‘yan makarantan gwamnati da ake ba abinci kyauta a firamare.

Tun kwanakin baya kun ji cewa Ministar jin kai da bada agajin gaggawa ta kasa, ta ce za a kara adadin masu shiga N-Power, GEEP, da ci da ‘Yan Makaranta.

Nan da shekaru 10 masu zuwa, shugaban Najeriyar yaci burin raba mutane miliyan 100 daga kangin talauci don haka ne ya fadada manufofin gwamnatinsa.

Sadiya Umar Farouk ta bayyana wannan a lokacin da tayi hira da Manema labarai a Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng