Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba saboda son farantawa wasu rai, Lawan

Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba saboda son farantawa wasu rai, Lawan

- Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya ce ba za su yaki Buhari ba saboda farin cikin wasu

- Lawan ya ce duk da yadda ake kira Buhari ya sallami shugabannin tsaro, suna iyakar kokarinsu wurin shawo kan matsalar tsaron

- Ya ce cigaban da ake samu a cikin kwanakin nan yana nuna yadda a hankali zaman lafiya zai dawo kasar nan

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a jiya ya ce majalisar tarayya bata da dalilin da zai sa ta yaki shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda tana son farantawa wasu rai a kasar nan.

Lawan ya sanar da hakan ne a yayin da ya karbar wakilai daga jihar Adamawa wadanda suka ziyarcesa domin nuna jin dadi ga majalisar tarayya a kan yadda ta sauya jami'ar Modibbo Adama da ke Yola.

Wakilan sun samu jagorancin Sanata Aishatu dahiru Ahmed da kuma shugaban jami'ar, farfesa Abdullahi Lima Tukur, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya harbi farar hula 4

Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba don farin cikin wasu, Lawan
Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba don farin cikin wasu, Lawan. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Lawan ya ce: "Idan bamu amince ba, za mu bayyana. Amma idan babu dalili ba za mu ki amincewa ba. Ba za mu yi abu ba domin farantawa wasu rai."

Idan za a tuna, sanatoci da 'yan Najeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami hafsoshin tsaro saboda yadda suka gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar Najeriya, lamarin da Buhari ya ki aikatawa.

Lawan ya jinjinawa hukumomin tsaron kasar nan ta yadda suke kokarin wanzar da zaman lafiya a sassan Najeriya, ya ce duk da yadda rashin tsaro ya tsananta, a hankali ana shawo kan hakan.

Ya kara da cewa, cigaban da ake samu a cikin kwanakin nan yana nuna kokarin da hukumomin tsaro ke yi wurin dakile rashin tsaron.

KU KARANTA: Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar

A wani labari na daban, Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom, Udo Ekpenyong ya rasu.

Ekpenyong ya rasu a ranar Litinin a Uyo kamar yadda wani jami'in gwamnatin jihar Akwa Ibom ya tabbatarwa da Premium Times a ranar Talata da safe.

Jami'in wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce shugaban jam'iyyar PDP din ya rasu ne sakamakon fama da yayi da cutar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel