2023: Daga karshe tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan batun dawowarsa kujerar

2023: Daga karshe tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan batun dawowarsa kujerar

- Jam’iyyar PDP ta yi martani ga rade-radin aminci da ke tsakanin Goodluck Jonathan da mambobbin APC

- Har yanzu babu tabbass a kan shirin da tsohon Shugaban kasar ke yi a siyasance gabannin zaben 2023

- Jam’iyyar adawar na fatan lashe zaben Shugaban kasa a 2023

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya jadadda cewa yayi wuri da za a fara tattauna yadda zaben 2023 zai kasance.

A cewar jaridar The Nation, tsohon Shugaban kasar yak an bayar da irin wannan amsar a duk lokaccin da aka tambaye shi ko yana da wani shiri da yake na takarar zaben Shugaban kasa na gaba.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa kyakkyawar alakar da ke bunkasa a tsakanin Jonathan da wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na haddasa fargaba a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

2023: Daga karshe tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi maagana kan batun dawowarsa kujerar
2023: Daga karshe tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan batun dawowarsa kujerar Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Rochas: Manyan jam'iyyun Nigeria basu da wani tsari bayan na cin zabe

Kafar labaran ta yi ikirarin cewa hankalin yan PDP bai kwanta da yawan ziyarar da tsohon Shugaban kasar ke kaiwa fadar Shugaban kasa ba a yan baya bayan nan.

Ta ce jam’iyyar ta shiga duhu cewa a lokacin da ya kai irin wannan ziyarar na karshe a ranar 15 ga watan Disamba, daga Jonathan har fadar Shugaban kasa abu wanda yace uffan game da dalilin ziyarar tsohon Shugaban kasar.

An kuma ce jam’iyyar adawar ta damu da rade-radin cewa APC na duba yiwar ba tsohon Shugaban kasar tikitinta na takarar Shugaban kasa a 2023.

Sai dai, Jonathan ya ki cewa uffan a kan kusancinsa da jam’iyyar mai mulki da rade-radin kudirinsa na takarar Shugaban kasa a 2023.

KU KARANTA KUMA: Dattijo mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33

A wani labarin kuma, wata hadimar Gwamnan jihar Ebonyi tayi murabus daga gwamnatin.

Hadimar wacce kafin murabus dinta take a matsayin babbar mai bayar da shawara ga gwamnan kan ci gaban kasuwanci ta bayyana dalilinta na ficewa daga gwamnatin.

A wasikar murabus dinta mai kwanan wata Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, wanda Legit.ng ta gano, Deaconness Udeakaji ta bayyana cewa murabus din nata ya zama dole domin tsiratar da aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng