Zamfara: Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24

Zamfara: Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24

- Sojojin Najeriya sun kashe tsageru a yankunan Bungudu da Muradun a Zamfara

- Dakarun Operation Hadarin Daji sun ga bayan Miyagun ‘Yan bindiga sama da 30

- DHQ ta bada wannan sanarwa a Gusau ta bakin Janar John Enenche ranar Litinin

A ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu, 2021, rundunar sojojin Operation Hadarin Daji suka kashe ‘yan bindiga 35 a jihar Zamfara inji jaridar Punch.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar sun yi nasarar karbe wasu dabbobi da miyagun suka sace.

Babban jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a Gusau, jihar Zamfara.

John Enenche yace: “Bayan samun bayanai game da sawun ‘yan bindiga dauke da dabbobin sata a Bungudu, jihar Zamfara, sojojin da ke Kekuwuje sun yi wuf, sun auka masu.”

KU KARANTA: Sojoji sun kashe 'Yan bindiga 50 a jihar Zamfara

A wajen wannan arba, an hallaka ‘yan bindiga 30, yayin da aka karbo shanu 24, da tarin tumaki.”

Jami’in ya kara da cewa: “Haka zalika duka a wannan rana (17 ga watan Junairu), sojojin da ke Maradun sun samu labarin harin da aka sake kai wa a Janbako, Zamfara.”

“Dakaru sunyi maza-maza su kai farmaki domin dakile harin. An yi masu kwantan bauna daf da dajin Janbako inda aka gwabza.” Inji Manjo Janar John Enenche

“Dakarun sojoji sun sha karfin miyagun, suka hallaka biyar daga cikinsu. Yanzu haka ana neman ragowar wadanda suka tsere."

Zamfara: Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24
COAS, Janar Tukur Yusuf Buratai Hoto: Twitter Daga: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakaru sun ceto wasu mutanen da aka sace a Zamfara

Sojoji sun kuma yi nasarar damke wasu mutane biyu da ke hada-kai da ‘yan bindigan Zamfara.

Janar John Enenche a madadin sojojin Najeriya, ya tabbatar da cewa dakaru za su cigaba da lallasa masu tada kafar-baya da sauran makiyan kasa, har sai an sau zaman lafiya.

A baya kun ji cewa 'yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da laifin tada tarzoma a jihar Zamfara. Lamarin da har ya kai ga jawo asara a fadar Sarkin Shinkafi.

Rahotanni sun ce wannan jawabi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.

Wasu tsageru dauke da bindigogi da adduna da sanduna sun kai wa fadar Sarkin Shinkafi hari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel