Rochas: Manyan jam'iyyun Nigeria basu da wani tsari bayan na cin zabe

Rochas: Manyan jam'iyyun Nigeria basu da wani tsari bayan na cin zabe

- Sanata Rochas Okorocha ya ce zasu ƙirƙira sabuwar tafiyar siyasa nan bada jimawa ba.

- Okorocha ya bayyana hakan ne a ranar litinin 18 ga watan Junairuɓln 2021.

- Tsohon gwamnan na jihar Imo jam'iyyar APC da PDP sun kada ƴan Najeriya ƙasa wanwar

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha wanda Sanata ne mai ci a halin yanzu, ya ce da shi da sauran ƴan siyasa masu son cigaban al'umma suna ƙirƙirar wata sabuwar tafiyar siyasa don tunkarar babban zaɓen 2023 da ke ƙaratowa.

Ya ce zasu yi hakan ne bisa yawan ƙorafe ƙorafe akan mawuyacin halin da ƙasa ta faɗa ciki.

The Nation ta tattaro maganar Okorocha a jawabinsa na ranar Litinin 18 ga watan Junairu 2021 inda ya ce;

"Mutane basu gamsu da irin mulkin kama karya da ake yi musu ba, akwai buƙatar "nagartattun ƴan siyasa" su tattara kansu wuri guda don gyara da farfaɗo da lamurra da kuma ceto ƙasa daga halin ƙaƙa ni kayi"

Rochas Okorocha ya ce akwai ɓatagarin mutane daga dukkan jam'iyyun PDP da APC.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Okorocha wanda ya ke wakiltar Kudancin Imo (Imo West) ya yi kira ga nagartattun ƴan siyasa daga jam'iyyun APC da PDP da su zo su haɗa kansu wuri guda don ceto ƙasa daga mayuwacin halin da ta shiga a babban zaɓen 2023.

Rochas: Manyan jam'iyyun Nigeria basu da wani tsari bayan na cin zabe
Rochas: Manyan jam'iyyun Nigeria basu da wani tsari bayan na cin zabe
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya ce akwai buƙatar sauya yanayin tafiyar siyasar ƙasar nan,ya yi gargaɗin cewa lokacin cigaba da rainawa ƴan Najeriya hankali ya wuce daga gurɓattun ƴan siyasa a shekarar 2023.

A jawabinsa, ya ce "Tafiyar sabuwar Najeriya ta fara, kuma dole mu dunƙule wuri guda,ina nufin nagartattun ƴan ƙasa don kawowa ƙasa cigaban da ake buƙata."

Sai dai Okorocha ya ce an yi jam'iyyar APC cikin gaggawa da hanzari don ƙwatar mulki daga hannun jam'iyyar PDP, ba tare da tantance halayyar wanda zasu jagorance ta ba.

KARANTA: Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Teti, shekara fiye da 2,500 baya

Ya tabbatar da cewa haɗakar tafiyar su zata tafi da nagartattun ƴan siyasa masu kyakkyawan tarihin kawo sauyi da kishin al'ummar su ba zulamammu masu haɗamar mulki ba.

"Ba zamu bar gurɓatattun ƴan siyasa marasa kishin al'ummar su shiga cikin tafiyar siyasar mu ba," a cewarsa.

Legit.ng ta rawaito cewa wata kungiya mai lakabin UGPRO ta sake shigar da karar Yakubu Dogara a gaban kotun tarayya da ke Abuja

A ranar Litinin ne kotun ta saurari karar da jam'iyyar PDP ta shigar da Dogara tare da bayyana cewa yanzu ba mamba bane a cikinta.

Dukkan masu karar na neman kotun ta tsige Dogara saboda ya samu nasara ne a karkashin inuwar jam'iyyarsu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel