Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa

- Allah ya yi wa Alhaji Bashir Aminu, Iyan Zazzau rasuwa

- Alhaji Bashir Aminu ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi

- Ya rasu a safiyar yau Juma'a, 1 ga watan Janairun 2021 a gidansa da ke Legas

Daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma. A yau safiyar 1 ga watan Janairun 2021 ne kasar Zazzau ta tashi da alhini tare da tashin hankali.

Hakan ya faru ne sakamakon rasuwar Alhaji Bashir Aminu, mai sarautar Iyan Zazzau a masarautar Zazzau.

Alhaji Bashir Aminu ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita.

KU KARANTA: Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa. Hoto daga Haleema Khalid
Asali: Facebook

Alhaji Bashir Aminu shine dan takarar kujerar sarautar Zazzau daga gidan Katsinawa.

Hakazalika, shine ya samu kuri'u uku daga cikin kuri'u biyar na 'yan majalisar nadin sarautar Zazzau suka saka.

Kamar yadda wani na hannun damansa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa da Legit.ng, ya ce Iyan Zazzau ya rasu a gidansa ne dake jihar Legas.

Allah ya ji kan shi da gafara. Ameen.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC

A wani labari na daban, mazauna karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro bayan sace 'yan mata uku da mayakan Boko Haram suka yi.

Madagali tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da mayakan Boko Haram suka kwace a 2014 kafin sojin Najeriya su kwato su a 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan mata biyu tare da matar aure daya ne ke aiki a gona a makon da ya gabata a wani kauyen Dar yayin da wasu mutane dauke da makamai suka cafkesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: