Sarkin Zazzau ya yi sabbin nade-nadensa na farko, ya yi sauye-sauye (jerinsu)

Sarkin Zazzau ya yi sabbin nade-nadensa na farko, ya yi sauye-sauye (jerinsu)

- Sarkin Zazzau na maye gurbin Iyan Zazzau da ya rasu makon da ya gabata

- Sarkin ya nada kaninsa domin maye kujerar sarautar gidansu da mahaifinsa ya rike

- Wannan ya biyo bayan rasuwar Iyan Zazzau, Bashar Aminu, a jihar Legas

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi sabbin nade-nadensa na farko kuma ya karawa wasu masu saurauta matsayi a masarautarsa.

An nada Bamalli sarkin Zazzau ranar 7 ga Oktoba, 2020, sakamakon mutuwar Sarki Shehu Idris ranar 20 ga Satumba, 2020.

A jawabin da masarautar ta saki, Sarkin ya maye gurbin marigayi Iyan Zazzau, Aminu Bashar, da dan majalisa mai wakiltan mazabar Zaria, Abbas Tajudden.

Hakazalika, Bammali, ya nada dan'uwasa, Mansur Bamalli, matsayin Magajin Garin Zazzau.

Ga jerin sabbin nade-naden:

1. Malam Mansur Nuhu Bamalli - Magajin Garin Zazzau.

2. Abbas Tajjuddeen - Iyan Zazzau.

3. Malam Shehu Tijjani Àliyu Dan Sidi Bamalli - Barde Zazzau.

4. Malam Abdulkarim Bashari Aminu - Talban Zazzau.

5. Malam Buhari Ciroma Aminu - Barde Kerarriyan Zazzau.

6. Alhaji Idris Ibrahim Idris - Sa’in Zazzau.

7. Alhaji Aminu Iya Saidu - Kogunan Zazzau

8. Alhaji Bashir Abubakar - Barden Kudun Zazzau

9. Justice Munnir Ladan - Dan Iyan Zazzau.

DUBA NAN: Kwamishanar lafiyan jihar Kaduna ta kamu da cutar Korona

Sarkin Zazzau ya yi sabbin nade-nadensa na farko, ya yi sauye-sauye (jerinsu)
Sarkin Zazzau ya yi sabbin nade-nadensa na farko, ya yi sauye-sauye (jerinsu)
Source: Twitter

KU KARANTA: Katin zama dan kasa: Duk laifin yan Najeriya, mu canza halin mu, Minista Pantami

Kun ji cewa dan rikon marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, ya yi watsi da jita-jitan da ke yawo na cewa kashe marigayi yariman Zazzau wanda ke shari’a da gwamnatin jihar Kaduna kan zabar sarkin Zazzau na 19 aka yi.

Legit.ng ta samu labarin rasuwar Aminu a jihar Lagas a safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu.

An dauki gawarsa zuwa Sabon Gari, jihar Kaduna, a ranar Asabar inda aka yi sallar jana’izarsa a masallacin Juma’ar da ke yankin kafin aka binne shi a gidansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel