NDLEA ta na neman mutumin da ya shigo da hodar iblis 21kg ta filin jirgin sama
- Hukumar NDLEA mai yaki da fasa-kauri da amfani da miyagun kwayoyi ta yi wani babban kamu
- Jami’an NDLEA sun tare wani kilo 21.9 na hodar iblis da aka yi yunkurin shigowa da shi ta jirgi
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata cewa jami’an hukumar mai yaki da miyagun kwayoyi sun yi kamun da ba su taba yin irinsa a lokaci guda ba.
Rahoton ya ce NDLEA tayi nasarar dakile wannan mugun kwaya ne a babban filin tashi da saukar jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke birnin tarayya Abuja.
A ranar 18 ga watan Junairu, 2021, Mai magana da yawun hukumar, Jonah Achema, ya bayyana cewa sun cafke wasu akwatuna biyu masu dauke da hodar Iblis.
Mista Jonah Achema ya ce hukumar ba ta taba tare kaya masu irin wannan yawa a lokaci guda ba.
KU KARANTA: Sabuwar kungiyar ‘yan dunkule hannu’ ta raba soyayyar shekaru 4
A cewar jami’in, an gano wannan kaya ne a cikin wasu akwatuna da aka bari a jirgin Ethiopian Airline, ET 910, wanda ya taho daga Addis Ababa, kasar Habasha.
“Da ake binciken jirgin, jami’an da ke lura sun zargi cewa akwai barnar da ake shirin yi bayan sun hangi akwatuna a ajiye ba tare da wani ya na ikirarin na sa bane.”
Jonah Achema ya cigaba da cewa: “Shugaban NDLEA ya sanar da ma’aikata su sa ido a kan kayan, kuma aka sanar da jirgin cewa hukuma ta na lura da akwatunan.”
“Bayan an yi kwanaki babu wanda ya fito ya ce shi ya mallaki kayan, shugaban NDLEA ya tuntubi ma’aikatan jirgin, ya bada umarni ka da a bada kayan sai a gabansu.”
KU KARANTA: An dakatar da daukar jami'ai 5,000 aiki a hukumar NDLEA
A karshe dole aka bude wadannan akwati domin a tabbatar da abin da yake ciki, sai ga hodar iblis (mai nauyin 21.9kg), wasu boye a wata leda da aka kudundune a bargo.
An yi wa kayan tas ne a gaban jami’an NCS masu yaki da fasa-kauri da DSS masu fararen kaya, da ma’aikatan harkokin jirgin sama, yanzu ana binciken mai wannan kaya.
Kwanan nan aka ji shugaba Muhammadu Buhari ya nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA.
Tsohon gwamna kuma sojan kasa, Mohammed Buba Marwa mai shekaru 67 ya zama sabon Darakta-Janar na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi na kasa.
Kafin yanzu, Marwa ya kasance shugaban kwamitin sugaban kasa na yaki da miyagun kwayoyi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng