SMAN: Wata ta rabu da Saurayinta saboda ya shiga kungiyar Matsolai a Kano

SMAN: Wata ta rabu da Saurayinta saboda ya shiga kungiyar Matsolai a Kano

- Kungiyar Stingy Men Association ta raba wani saurayi da sahibarsa

- Buduwarsa ta rabu da shi bayan ya shiga wannan sabuwar kungiya

- Wadannan mutane sun shafe shekaru har hudu suna soyayya a Kano

Wasu Bayin Allah da suka shafe tsawon shekaru hudu suna soyayya a Kano, sun rabu a sanadiyyar shigar saurayin sabuwar kungiyar nan ta matsolai.

Wannan matashi ya yi amfani da shafinsa na Facebook, ya sanar da Duniya cewa ya karbi kiran kungiyar Stingy Men Association of Nigeria (SMAN).

Jaridar Sahelian Times ta fitar da wannan rahoto a ranar Juma’a, 16 ga watan Junairu, 2021, ta ce sunan matashin Muzammil.

Muzammil ya shaidawa jaridar a wata tattaunawa da tayi da shi cewa abin ya fara kamar da wasa, buduwarsa ta kira sa tana kokawa da matakin da ya dauka.

KU KARANTA: Hotunan Buhari ya na rabon kudi ya jawo surutu

Budurwar da ba ta bari an bayyana sunanta ba, ta fada wa Malam Muzammil ba za ta iya cigaba da soyayya da shi batun da ya shiga wannan kungiya.

A cewar Budurwar, ba za ta iya cigaba da tarayya da mutumin da ya shiga kungiyar da aikinta da manufofinta ya ci karo da koyarwar addinin musulunci ba.

Wannan budurwa ta ce duk mai dabi’ar rowa, abin da kungiyar ta yi fice a kai, ba zai shiga Aljanna a gobe kiyama ba, ta ce wannan ya sa ta rabu da Muzammil

“Addinin musulunci sam, ba ya goyon-bayan rowa. Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gareSa, ya ce duk marowaci ba zai shiga aljanna ba.”

KU KARANTA: Dino Melaye ya na rawan wakar kungiyar masu dunkule hannu

SMAN: Wata ta rabu da Saurayinta saboda ya shiga kungiyar Matsolai a Kano
Kungiyar masu dunkule hannu Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Yanzu dai wannan soyayya ta shekaru hudu ta zo karshe a sakamakon biyewa kungiyar Stingy Men Association of Nigeria ta matsolai da saurayin ya yi.

A makon da ya wuce ne muka ji cewa bayan Nigeria, an bude kungiyar nan samari masu 'dunƙule hannu' a wasu kasashe biyar a Nahiyar Afrika.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu. Wadannan kasashen sun hada har da Ghana.

Ragowar kasashen da kungiyar ta bulla su ne: Liberiya, Uganda, Malawi da kuma Zambiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel