FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA

FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA

- Barkewar annobar korona na biyu a Najeriya ya dakatar da shirin daukar mutum 5,000 a hukumar NDLEA

- AGF Malami, wanda yayi umurnin dakatar da lamarin na wucin gadi, ya ce aiwatar da shirin zai saba yarjejeniyar COVID-19

- Ministan shari’an ya umurci jami’an shirin da su nemi bayanan da ya kamata kafin su ci gaba da shirin daukar ma’aikatan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin daukar ma’aikata 5,000 a hukumar yaki da hana fatauci da shan miyagun kwayoyi (NDLEA).

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Atoni Janar na tarayya (AGF), Abubakar Malami ne ya dakatar da shirin daukar ma’aikatan.

Malami ya bayyana cewa ci gaba da shirin daukar ma’aikatan na NDLEA zai hada da tattara mutane da dama a waje guda. Wannan, a cewarsa zai saba yarjejeniyar COVID-19 na kasa.

FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA
FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA Hoto: @MalamiSan
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ragakafin korona: Buhari ya ce ayi wa manyan mawaka, Limamai da fastoci allurar kai tsaye ta akwatin talbijin kowa ya gani

Ministan shari’an ya ce yayin da shirin daukar ma’aikatan ya dade da yi da kuma bukatar aiwatar da umurnin hukumar, ya zama dole a magance matsalar halin da tsaron lafiya ke ciki.

A wata sanarwa daga ofishin Malami, ya bukaci wadanda ke da alhakin daukar ma’aikatan da su:

“Nemi bayani/shawara daga kwamitin fadar Shugaban kasa kan korona kan illar da irin wannan shiri ke da shi ga lafiyar al’umma musamman ta bangaren bin ka’i’ojin cutar korona.”

Ofishin Malami ya ce ya damu da ganin cewa an umurci wadanda suka yi nasara da su tattaru a akarantar NDLEA, Citadel Counter-Narcotics Nigeria, (CCNN), Katton-Rikkos a Jos, jihar Plateau.

KU KARANTA KUMA: Rarara ya gwangwaje jaruman Kannywood da kyautar sabbin motocin alfarma

A baya mun ji cewa hukumar Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara cikin masu neman shiga aiki a hukumar.

Mai magana da yawun rundunar, DCN Jonah Achema ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma'a a Abuja, News Wire ta ruwaito.

Ya ce wadanda suka nemi shiga aikin su ziyarci shafin yanar gizo ta hukumar a www.ndlea.gov.org domin ganin jerin sunayen wadanda suka yi nasara, ya kara da cewa an kuma aike musu sakon tes de imel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel