Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirin rushe hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da takwararta ICPC

- Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar Buhari a zauren majalisar, mai taken: "Dokar hukumar gurbattun kudade"

- Sabuwar hukumar za ta tabbata 'yan Nigeria sun amfana da kudaden da aka kwato daga mahandaman kasar, ba tare da boye boye ba

A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirin ruguza hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: "Dokar hukumar gurbattun kudade".

Ahmad Lawan ya ce sabuwar dokar za ta magance matsalar rufa rufa da ake yi wajen alkinta kudaden da hukumomin biyu ke kwatowa daga barayin kasa.

KARANTA WANNAN: 'Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen maganin ciwon idanu'

Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili
Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili - @daily_trust
Asali: Twitter

Buhari a cikin wasikar ya bayyana cewa aikewa majalisar dattijai bukatar rushe hukumomin da samar da sabuwar dokar ya samu sahalewar majalisar zartaswa ta kasa.

A cewar wasikar da aka aikata a ranar 6 ga watan Oktoba, sabuwar dokar hukumar zai tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa, safarar kudade ba bisa ka'ida ba da sauran laifuka.

"Muhimmancin dokar shine kirkirar hukumar yaki da gurbatattun kudade (alkinta kudaden da aka kwato).

"Manufofin hukumar shine sa ido kan dokar da kuma yin ruwa da tsaki a alkinta kudaden da aka kwato daga barayin kasa ta hanyar hadin kai da hukumomin tsaro.

"Sannan abu mai muhimmanci shine, hukumar za ta tabbata 'yan Nigeria sun amfana da kudaden da aka kwato daga mahandaman kasar, ba tare da boye boye ba."

KARANTA WANNAN: An sace matar wani babban dan jarida a Calabar

Idan har aka amince da wannan doka, za ta taimaka wajen dakatar da EFCC da sauran hukumomin yaki da rashawa guda 6 daga rufe asusun mutanen da ake bincika.

Sauran hukumomin sun hada da hukumar ICPC, NDLEA, NFIU, NAPTIP, CCB da kuma rundunar 'yan sandan Nigeria," a cewar shugaban majalisar dattijan.

A shekarar da ta gabata tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ne ya amince da dokar, sai dai tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya nuna rashin amincewa da dokar.

A wani labarin, Olaniyan, wanda ya shiga sahun dubunnan masu zanga zanga a kofar shiga babbar sakatariyar gwamnatin jihar Oyo, Agodi Ibadan, ya yi kira da a kawo karshen zaluncin 'yan sanda.

Mataimakin gwamnan, wanda ya shiga sahun masu zanga zangar yana dauke da allon kwali a kofar shiga sakatariyar, ya ce sau biyu jami'an SARS suna cin zarafin sa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel