CAN ga Zulum: Kiristoci basa ta’addanci, Boko Haram sun bayyana akidarsu

CAN ga Zulum: Kiristoci basa ta’addanci, Boko Haram sun bayyana akidarsu

- Furucin da Gwamna Babagana Zulum yayi kwanan nan ya haddasa zazzafan martani daga wasu Kiristoci

- Gwamnan na jihar Borno ya yi ikirarin cewa wasu Kiristoci na cikin mambobin kungiyar ta’addanci na Boko Haram

- Da dama sun yi watsi da ikirarin gwamnan sannan suka bukaci ya gabatar da hujja kan ikirarinsa

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi watsi da ikirarin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, wanda ya bayyana cewa wasu Kiristoci na cikin yan Boko Haram.

Babban sakataren kungiyar CAN, Joseph Daramola, ya fada ma jaridar Punch a wata hira a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu, cewa Kiristoci ba za su taba kasancewa cikin yan ta’addan ba saboda kungiyar na danganta kanta da addinin Islama ne a koda yaushe.

Daramola ya gargadi gwamnan da ya daina zargin, inda ya kara da cewa kungiyar ta nuna akidarta a bidiyo da dama.

CAN ga Zulum: Kiristoci basa ta’addanci, Boko Haram sun bayyana akidarsu
CAN ga Zulum: Kiristoci basa ta’addanci, Boko Haram sun bayyana akidarsu Hoto: @GuardianNigeria
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP (bidiyo)

“Ubangiji ya yi umurnin cewa kada wanda yayi kisa kuma kaima kada kayi kisa imma a gaba-da-gaba ko ta wani siga. Kiristocin da suke Kiristoci na hakika ba za su taba aikata haka ba. Idan Zulum na da hujjojinsa, toh ya fito da su.”

Kafin kungiyar CAN tayi martani kan ikirarin Zulum, yan Najeriya da dama sun yi ta watsi da furucin gwamnan.

Kingsley Ekwa ya rubuta a Twitter:

“Wato Zulum ya ga mambobin kungiyar Boko Haram sannan ya tattauna da su don gano cewa akwai Kiristoci da bakin haure a cikin Boko Haram. Dole yana da nasaba da Boko Haram. Mutanen da ke yiwa kungiyar Islama yaki kiristoci ne, shin wannan ba abun dariya bane?”

Tsohon hadimin tsohon Shugaban kasa kuma Fasto, Remo Omokri ma ya rubuta:

“Ya zama dole Gwamna Zulum ya bayyana hujjarcewa Kiristoci yan Boko Haram ne. Dole Zulum ya gabatar da hujja ko ya bayar da hakuri.”

Nekka Smith ya rubuta:

“Idan Farfesa Zulum na da bayanai a kan addini da kabilar yan kungiyar Boko Haram, toh dan Allah hukumar DSS ta gayyace shi don yi masa tambayoyi domin yayi magana karara kan ikirarinsa.”

KU KARANTA KUMA: COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria

A baya mun ji cewa Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina ganin fitinar da ke faruwa a jihohin arewa maso gabashin jihohin Borno, Yobe da Adamawa a matsayin matsalar arewa; kalubale ne da ya shafi kowa da kowa.

Zulum ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani na shekara ta 17 na Gani Fawehinmi wanda Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, reshen Ikeja ta shirya ranar Juma’a.

A cewarsa, mambobin kungiyar ta Boko Haram sun hada da fararen fata, 'yan Asiya, 'yan Afirka, Musulmai da Kirista, Sahara Reporters ta ruwaito.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel