COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria

COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria

- Kwamitin fadar shugaban kasa kan COVID-19 ta gargadi yan Najeriya a kan tursasa FG sake sanya dokar kulle a kasar

- Boss Mustapha, shugaban PTF, ya yi gargadin a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu a Abuja

- Sai dai, Mustapha ya bayyana cewa hukuncin gwamnati zai ta’allaka ne a kan bin dokokin mutane

Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Najeriya da su yi duk abunda za su iya don guje ma rufe Najeriya a karo na biyu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan korona, Boss Mustapha ne yayi wannan rokon a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu, a wani taron manema labarai.

Legit.ng ta tattaro cewa Mustapha, wanda ya kuma kasance sakataren gwamnatin tarayya, ya ce hakan zai kasance ne ta hanyar bin ka’idojin da gwamnati ta saki.

COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria
COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria Hoto: @DigiCommsNG
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Buhari ya amince da nadin Nuhu Fikpo a matsayin shugaban riko na NDE

Mustapha ya ce gwamnati na kokari ta bangaren kula da lamarin ta hanyar samun tallafin ma’aikatu masu zaman kansu wajen samar da iskar shaka a hukumomi daban daban.

Ya ce:

“Bari na tunatar da ku cewa annobar na hauhawa kuma ya zama dole gwamnati da yan kasa su hada hannayensu.

“Muna cikin mawuyacin hali da ya zama dole a ci gaba da buga-buga tsakanin rayuwa da abubuwan tafiyar da rayuwar. Muna duba yiwuwar daukar duk wani mataki yayinda muke sanya ran samun hadin kai sosai. Ya zama dole muyi duk abunda ya kamata domin guje ma yiwuwar rufe Najeriya a karo na biyu."

KU KARANTA KUMA: Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka

A gefe guda, wani rahoto daga kafar yaɗa labarai ta ƙasar Sin, an gano samfura uku na alawar ice cream sun gurbata da ƙwayar cutar COVID-19 a yankin Tianjin da ke arewa maso gabashin kasar Sin.

Kimanin kwalaye 4,836 na ice cream ɗin ne wanda kamfanin abinci na Tianjin Daqiaodao ya samar amma aka ce cakuɗe suke da ƙwayar cutar COVID-19, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Yanzu haka an datse robobi 2,089 na alawar ta 'Ice Cream' bayan gano kwayar cutar a cikinsu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel