Soyayya da mai mata kamar tuwo ba miya ne saboda ba kiran tsakar dare, ba na sassafe sai in ya saci fita, in ji budurwa
- Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cecee-kuce a shafin Twitter bayan ta bayar da wani shawara a kan soyayya da mai mata
- Budurwar @ayeesh_chuchu ta ce soyayya da mai mata akwai takura sosai tamkar tuwo gaya ba miya ne
- A cewar matashiyar, daga cikin illar soyayya da mai mata shine ba za ku samu damar yin wayar tsakar dare da na sassafe ba, babu sakon tex na tsakar dare sai idan ya saci jiki
Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @ayeesh_chuchu ta bayyana cewa soyayya da namiji mai mata yana da tarin takura da tauye romon jin dadin soyayyar.
@ayeesh_chuchu ta bayyana cewa irin wannan soyayya tamkar gayar tuwo babu miya ne saboda mutum ba zai samu cikakken lokacin kasancewa tare da masoyin nasa ba sai dai idan ya yi nisa da iyalinsa.
Ta ce a irin wannan soyayyar, mutum ba zai samu damar hira da masoyin nasa ta waya ba a tsakar dare da kuma sassafe. Sannan ta ce ko sakon tex mutum ba zai iya aikawa bad a tsakar dare.
Ta kuma bayyana cewa lokaci guda da mutum zai samu sararin kasance da shi shine idan baya tare da matarsa ta gida ko kuma idan ya fita yin wasu harkoki.
KU KARANTA KUMA: Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria
Ta ce: “Soyayya da mai mata na tattare da takura sosai wolla...Ehnn! babu wayan tsakar dare, babu kiran sassafe..Babu sakon tex na tsakar dare. Za ka kasance tare da shi ne kawai idan ya iya samun sarari daga iyalinsa ko kuma ya saci fita sannan ya hadu da ke. Gaya ne zalla kamar tuwo ba miya.”
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mabiya shafin a kasa:
@Bntabbas ta yi martani cewa
“Uzuri kamar; Zan je aski Bari in siyo Bread din safe, Zamu je ball, Zan karbo kayan wanki Etc”
@salmah_farouk ta ce:
“Wow ta yaya kika san wadannan abubuwan? Kina da aure ne.”
KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi 4, sun kwato shanu 200 da makamai a Zamfara
@Burhan_muksamad
“Hmn. Hakan na nufin ya san darajar matarshi ne, yake bata lokaci, kema ya baki naki daban, da ace baisan darajar matarshi ba, da waya zai dnga yi a gabanta dake. Imma ya kasance miji nagari ko kuma wanda matarsa ke juya shi."
@_Maymunatuu ta ce:
“Wllh ko haka ne. Amma sunfi sanin darajar Ki.”
@jimada_ibm ya ce:
“Idan ke kika tsinci kanki a matsayin matar namiji mai aure, zaki so mijinki ya aikata wadannan abubuwan da kika ambata da macen da bai riga ya aura ba? Ki kara hakuri, idan ya auree ki, za ku samu lokacin da kuke bukata a tare cikin kwanciyar hankali bisa halali."
A wani labarin, wata matashiyar yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @Mareeyarhh ta shawarci mata a kan su guji auren mazan Hausawa idan har suna son kwanciyar hankali a gidan aurensu.
Matashiyar budurwar bata tsaya a nan ba, ta kuma shawarci mata a kan su guji auren Mazan hausawa da suka fito daga Kano idan har suna son jin dadin aure.
Mutane da dama sun yi martani a wallafar da matashiyar tayi yayinda wasu da dama musamman maza suka caccake ta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng