Kamfanin takin Dangote ya tallafawa al'ummar Ibeju-Lekki

Kamfanin takin Dangote ya tallafawa al'ummar Ibeju-Lekki

- Kamfanin takin zamani na Dangote ya gina katafaren makaranta a jihar Legas

- Mutanen Ijebu-Lekki sun nuna farin cikinsu da jin dadi dangane da aikin da kamfanin ya yi musu

- Kamfanin ya jaddada cewa yana daga cikin aikinsu wanzar da ilimi tsakanin al'ummar kasar baki daya

Kamfanin takin zamani na Dangote ya gina katafariyar dakin karatun zamani da miliyoyin naira na zamani tare da mika shi ga hukumar kula da ilimin bai-daya ta jihar Legas, Jaridar The Punch ta ruwaito

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi ta ce, gudummawar makarantar na da nufin samar wa al’ummar Abejoye da ke yankin Ibeju-Lekki na Legas ingantaccen ilimi ta hanyar samar da kayayyakin koyarwa da kuma yanayi mai kyau.

A cewar manajan kamfanin takin, ajujuwan da aka gina a matsayin wani bangare na kokarin daukar nauyin jama'a na kamfanin, za su yi aiki ne a madadin Makarantar Firamare ta Abejoye.

KU KARANTA: Rashin Tsaro: Buhari ya yi kira ga daukar matakin bai daya kan 'yan ta'adda

Makarantar tana daga cikin yankin kasuwanci na kyauta da aka ware wa DFL, amma an komar da ita zuwa ga al’ummar Abejoye, yanzu haka ta kunshi dakunan ma’aikata, ofishin shugaban malamai, wuraren bayan gida, injin samar da wutar lantarki da kuma rijiyar burtsatse.

Kamfanin takin Dangote ya tallafawa al'ummar Ibeju-Lekki
Kamfanin takin Dangote ya tallafawa al'ummar Ibeju-Lekki Credit: Business Day
Source: Facebook

Da yake jawabi a bikin mika kayan a Legas, Babban Daraktan Zartarwa, Strategy Capital Projects da Portfolio Development, Dangote Industries Limited, Devakumar Edwin, ya yi alkawarin kamfanin zai yi sadaukarwa domin samar da ingantaccen ilimi a kasar nan baki daya.

A cewarsa, Tallafin Dangote na ci gaban ilimi ya shafi taimaka wa al'ummomin da ke karbar bakunci don samar da ingantaccen ilimi mai inganci wanda daga karshe zai isa ga dukkan mutane.

Ya ce, “Mu a matsayinmu na kamfani mun yi imanin cewa ilimi fasfo ne na nan gaba kuma cewa saka hannun jari a cikin ilimi shine mafi kyawu kuma muna da muradin haɓakawa, ilimantarwa da kuma ƙarfafawa matasa.

"Muna cimma wadannan manufofi ne ta hanyoyi daban-daban kamar bayar da tallafin karatu ga dalibai 50 da aka zaba a tsakanin al'ummomin da ke karbar bakuncinmu, tare da horar da matasa 200 kan sana'o'in hannu da dama."

Edwin ya kara da cewa kamfanin ya fara shirye-shirye daban-daban da nufin bunkasa kananan hukumomi a tsakanin al'ummomin da suke karbar bakuncinsu don basu damar gudanar da ayyukansu na ci gaban kansu.

KU KARANTA: Nijeriya ta fi yadda ta kasance muni a shekaru 6 - Jigo a jam'iyyar APC

Shugaban zartarwa na LASUBEB, Wahab Alawiye-King, wanda Daraktan sashin aiyuka, Ebaide Omokore ya wakilta a taron, ya yaba wa kamfanin takin zamani na Dangote saboda samar da kayayyakin aiki don inganta ilimi.

Ya lura cewa hukumar tana kuma gudanar da ayyukan inganta kayayyakin more rayuwa da gyara a sassa da dama na jihar, musamman a tsakanin al'ummomin da ke da wahalar shiga.

Shima da yake magana a wurin taron, Shugaban Karamar Hukumar Lekki Local Council Development Area, na Jihar Legas, Ogidan Olaitan, ya yaba wa kamfanin bisa wannan karamcin, yana mai cewa kamfanin zamani na Dangote ya tabbatar da cewa kamfani ne mai kula da zamantakewar al'umma, wanda ke da sha'awar kamfanin a zuciyarsa.

A wani labarin, An yi taro cikin walwala da annashuwa yayinda Aziza Dangote ta auri burin ranta Aminu Waziri a wani yanayi da za a iya kira da hadadden biki.

Kyakkyawar amaryar ta kasance diya ga Sani Dangote, wanda ya kasance mataimakin Shugaban kamfanonin Dangote tare da yayansa, Aliko Dangote.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel