Rudani tare da rashin tabbaci tattare da mutuwar dan majalisar wakilai

Rudani tare da rashin tabbaci tattare da mutuwar dan majalisar wakilai

- An samu rudani dangane da mutuwar wani dan majalisa, Hon. Ossy Prestige dake wani asibiti a kasar Jamus

- Dama tun watan Oktoban 2020 aka tafi dashi asibitin, duk da dai ba a tabbatar da irin cutar da yake fama da ita ba

- Duk da dai matarsa ta tabbatar da cewa yana da rai, amma yana bangaren ICU ana cigaba da ba shi kulawa

An samu rudani a ranar Litinin dangane da mutuwar wani dan majalisar wakilai, Hon. Ossy Prestige, a wani asibiti dake kasar Jamus, The Nation ta wallafa hakan.

Prestige dan majalisa ne daga jihar Abia a karkashin jam'iyyar APGA. Tun watan Oktoban 2020 aka tafi dashi asibitin yana fama da cutar da ba a bayyana ba.

Sai dai an samu labari daga wurin matarsa cewa yana matsanancin yanayi a asibitin a ranar Lahadi, amma ba a tabbatar da mutuwarsa ba.

KU KARANTA: Koma: Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Najeriya

Dimuwa da rashin tabbaci tattare da mutuwar dan majalisar wakilai
Dimuwa da rashin tabbaci tattare da mutuwar dan majalisar wakilai. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Wata majiya ta ce: "Ba gaskiya bane batun mutuwarsa. Matarsa dai ta ce yana bangaren ICU, kamar yadda ta tabbatar wa da wani. Sai dai ana ta kiransa ta WhatsApp amma ba ya amsawa."

Sannan wata majiya daga ofishinsa dake Aba ta ce, yana nan da ransa amma ana cigaba da kulawa da shi.

An kira kakakin mai magana da yawun majalisar, Hon. Benjamin Kalu, amma bai daga wayarsa ba.

KU KARANTA: Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

A wani labari na daban, dan majalisar jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Kafin-Hausa, Adamu Babban Bare daga jam'iyyar APC ya rasu.

Shugaban kwamitin majalisar a fannin yada labarai, Aminu Zakaru Tsubut ne ya bayyana hakan a garin Dutse, Vanguard ta wallafa.

Ya ce cike da alhini majalisar ta samu labarin rasuwar mutum mai kishin kasa da kuma kwazo Aminu Zakari ya kwatanta rasuwar Babban Bare da babban rashi ba ga iyalansa ko majalisar jihar kadai ba, amma ga APC da dukkan jihar Jigawa baki daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel