Da duminsa: Allah ya yi wa dan majalisar jiha a Jigawa, Adamu Babban Bare, rasuwa

Da duminsa: Allah ya yi wa dan majalisar jiha a Jigawa, Adamu Babban Bare, rasuwa

- Allah ya yi wa dan majalisa a jihar Jigawa, Adamu Babban Bare, rasuwa

- Shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Kafin-Hausa a jihar Jigawa

- Ya rasu bayan doguwar jinyar cutar kansa da ta koda da yayi fama da su

Dan majalisar jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Kafin-Hausa, Adamu Babban Bare daga jam'iyyar APC ya rasu.

Shugaban kwamitin majalisar a fannin yada labarai, Aminu Zakaru Tsubut ne ya bayyana hakan a garin Dutse, Vanguard ta wallafa.

Ya ce cike da alhini majalisar ta samu labarin rasuwar mutum mai kishin kasa da kuma kwazo

Aminu Zakari ya kwatanta rasuwar Babban Bare da babban rashi ba ga iyalansa ko majalisar jihar kadai ba, amma ga APC da dukkan jihar Jigawa baki daya.

KU KARANTA: Koma: Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Najeriya

Da duminsa: Allah ya yi wa dan majalisa jiha a Jigawa, Adamu Babban Bare, rasuwa
Da duminsa: Allah ya yi wa dan majalisa jiha a Jigawa, Adamu Babban Bare, rasuwa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Mamacin ya rasu yana da shekaru 57 bayan doguwar jinyar rashin lafiya da aka alakanta da cutar kansa da kuma ciwon koda.

Za a birne shi kamar yadda addinin Islama ya tanadar a garinsa na Kafin-Hausa da karfe 11 na safe.

An zaba Babban Bare domin wakiltar mazabar Kafin-hausa a majalisar jihar a zaben 2019. Shi ne tsohon sakataren kramar hukumar Kafin-Hausa a jihar Jigawa.

KU KARANTA: Kano: An bai wa hammata iska tsakanin fasinjoji da jami'an kamfanin AZMAN

A wani labari na daban, an samu rikici a yammacin Juma'a a filin sauka da tashi na jiragen sama na Malam Aminu Kano bayan fasinjoji sun tada tarzoma sakamakon soke tashin jirgin yammacin na kamfanin Azman da aka yi.

Rikicin ya yi kamari wanda ya kai ga wata ma'aikaciyar kamfanin Azman ta yanke jiki ta fadi yayin tashin hankalin.

An bar wani fasinja cikin jini yayin da wani ma'aikacin kamfanin ya kusa tsirara bayan yagalgala masa kaya da aka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: