Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka

Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka

- Wani jajirtaccen dan Najeriya mazaunin Amurka ya yi niyyar share wa 'yan Najeriya kuka

- Mutumin, mai suna Henry I. Balogun ya kirkiri wata kafar yanar gizo don sada masu neman aiki da masu basu aikin yi

- Kafar ya ayyana ta cewa kyauta ne amfani da ita ba tare da biyan ko da anini ne ba

Wani Ba’amurke dan asalin kasar Najeriya, Dakta Henry Balogun, ya jagoranci wani dandalin yanar gizo don rage rashin aikin yi a Najeriya, ta hanyar neman guraben aiki a duniya, ga daliban da suka kammala karatun su na Najeriya.

Balogun, haifaffen Ikere dake Jihar Ekiti ne kuma ya zauna a Amurka sama da shekaru 40, ya ce yana bayar da ayyukan ne ba tare da karbar anini ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, kokarin na zuwa ne ta dandalinsa na yanar gizo, www.primehangout.com, wanda ke taimakawa wadanda suka kammala karatu, musamman wadanda suka fito daga Najeriya wadanda ke bukatar aiki, don samun abun yi.

KU KARANTA: Da duminsa: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona

Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka
Wani dan Najeriya ya kirkiri hanyar samawa matasa aiki a Amurka Hoto: The Nation
Source: UGC

Ya ce a wannan shekarar kadai, dandamalin nasa ya yi niyyar samar da ayyuka sama da miliyan 20 ga ‘yan Najeriya.

"Abin da kawai muke yi shi ne tattara bayanan mutane ne da kuma haɗa ku da ma'aikata waɗanda ke buƙatar ayyukanku," in ji shi.

Bayan haka, ya kuma bayyana cewa a yayin mummunan tasirin cutar COVID-19 a kan tsarin ilimin duniya, dandalin nasa ya tattara bayanan mutune kuma ya gudanar da jerin laccaci a yanar gizo don taimakawa dukkan nau'o'in ɗalibai.

Balogun, wanda shi ne wanda ya kirkiro da kuma samar da ajin, ya ce an ware ajujuwan ne ta yanar gizo domin ba da kulawa ta musamman ga bukatun daliban Afirka.

A cewar sa da yawa daga cikin daliban sun zama masu rauni, saboda nisantar jama'a da taro da Coronavirus ta haifar.

Ya ce, “Wannan wata fasaha ce da aka kirkira don taimakawa dalibai na kowane zamani a kokarinsu na daukaka ilimi da kuma ba da gudummawa ga duk wata cibiyar karatu a duk duniya.

KU KARANTA: Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN

"Ba za a iya jinkirta buƙatar ɗaukar wannan tunanin cikin sauri ba, idan aka yi la’akari da gaskiyar abin da ya faru na lalacewar tsarin ilimin duniya da Coronavirus; tare da Afirka kasancewa a karshen karbar," in ji shi.

A wani labarin daban, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rufe makarantu saboda annobar COVID-19 zai yi tasiri mara kyau a kan ci gaba, aminci da kuma lafiyar yara a duniya, yana mai lura da cewa makarantu ba direbobin cutar ba ne, The Punch ta ruwaito.

UNICEF ta kuma yi gargadin cewa sakamakon rufe makaranta har shekara guda za a ji shi har zuwa tsara mai zuwa.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata ta ci gaba da cewa duk da kwararan shaidu da ke nuna cewa makarantu ba direbobi ne na cutar ba, an dauki matakai don tabbatar da cewa sun kasance a rufe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel