Amotekun: Yadda Dakaru suka aika mutane 11 lahira a kwanaki 20 da suka wuce
- Dakarun Jihohin Kudu maso yamma sun kashe mutane 11 a Jihar Oyo
- Amotekun sunyi wannan aika-aikan ne a makonnin uku da su ka wuce
- Gwamnonin Yarbawa suka kafa Amotekun domin a kawo zaman lafiya
Ana jifan dakarun jami’an tsaron da gwamnoni suka kafa a jihohin Kudu maso yammacin Najeriya, WNSN, da laifin keta hakki da cin zarafin al’umma.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ana zargin sojojin Amotekun da hallaka Bayin Allah.
Tuni kungiyoyi da lauyoyi masu kare hakkin Bil Adama suka fara yin kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo karshen aika-aikan da Amotekun su ke yi.
Rahoton yace lamarin Amotekun ya na nema ya zo da matsala musamman a jihar Oyo, inda dakarun suke rike bindigogi da sauran makamai masu hadari.
KU KARANTA: Sojojin Amotekun sun kashe uba da 'ya'yansa biyu a Oyo
Mutane da-dama sun mutu a hannun na Amotekun, amma har yanzu gwamnonin yankin jihohin Kudu maso yammacin kasar suna kare danyen aikin dakarun.
Daga cikin wadanda wadannan jami'ai suka kashe har da wani abokin aikinsu da kuma wasu makiyaya, wanda kisan su ya jawo abin magana a yankin.
A ranar Laraba, 13 ga watan Junairu, 2021, jami'an sojojin Amotekun suka kashe wani Tosin Thomas mai shekaru 21 da ya ke karatu a garin Ibadan, jihar Oyo.
Jami’an ‘yan sanda na jihar Oyo ta bakin kakakinsu, Olugbenga Fadeyi, sun tabbatar da cewa Marigayi Tosin Thomas ya mutu ne a hannun sojojin Amotekun.
KU KARANTA: Amotekun: Gwamnatin Buhari da gwamnonin Kudu sun samu maslaha
Shugaban dakarun, Kanal Olayanju Olayinka (mai ritaya), ya tabbatar da wannan lamari, amma ya ce an mikawa jami’an tsaro wanda ya harbe matashin.
A jihar Oyo kawai, sojojin Amotekun sun kashe mutane 11 kenan a cikin mako uku da ya wuce.
A gefe guda kuma, kun ji labari sojojin Najeriya sun aika 'yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane fiye da 2, 000 lahira cikin watanni 9 a shekarar bara.
Bayan haka, Mr. Femi Adesina ya ce jami’an tsaro sun ceto mutane fiye da 800 da aka yi garkuwa da su daga tsakiyar watan Maris zuwa karshen shekarar 2020.
Hadimin shugban kasar ya bayyana nasarar da dakarun sojojin Najeriya suka samu a kan ‘yan ta’adda.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng