Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3

Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3

- Mutuwa mai yankar kauna ta sake dauke wani babban jami’in rundunar yan sandan Najeriya

- Yunana Babas, mataimakin Sufeto Janar na yan sanda, ya mutu

- Zuwa yanzu ba a yi cikakken bayani game da abunda ya haddasa mutuwarsa ba

Mataimakin babban sufeton rundunar yan sandan Najeriya, Yunana Babas ya rasu. Shine ke kula da Zone 8, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya rasu kwanaki uku bayan mutuwar wani mataimakin babban sufeton yan sanda, Omololu Bishi.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman, ya yi ta’aziyya ga hukumomin yan sanda a kan rashin da suka yi.

Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3
Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3 Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

Abdulrahman ya bayyana Babas a matsayin kamilin mutum kuma jajirtaccen jami’i.

“Na samu labarin mutuwar AIG Yunana Babas cikin dimuwa da bakin ciki.

KU KARANTA KUMA: Daukar ma’aikata: Farin ciki fal yayinda wani gwamna ya amince da daukar matasa 4,000 aiki

“A madadin mutane da gwamnatin jihar Kwara, ina ta’aziyya ga dukka ahlin dan sandan, musamman Sufeto Janar na yan sanda da iyalan babban jami’in.

“Marigayin ya kasance kamilin mutum, wanda ya taimaka wa kasa, kuma kwararren dan sanda wanda ke yiwa kasarsa hidima. Na tuna da rawar ganin da marigayin ya taka a wasu lamuran tsaro a yankin."

Gwamnan ya yi wa marigayin addu’an samun jin kai a wajen Allah da kuma ba iyalansa dangana.

A wani labarin, Sultan na Sokoto, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya rasa kaninsa, Abdulkadir Jeli Abubakar III.

PM News ta ruwaito cewa Jeli ya mutu a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu yana da shekaru 64 a duniya.

Legit.ng ta tattaro cewa Jeli, wanda ya kasance kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Sokoto, ya mutu bayan yayi fama da rashin lafiya.

Mai ba Gwamna Tambuwal shawara a kan labarai, Malam Muhammad Bello, ne ya tabbatar da mummunan labarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel