Abun bakin ciki yayinda Sultan na Sokoto ya rasa kaninsa Jeli
- Sultan Sa’ad Abubakar na Sokoto ya shiga alhini
- Shugaban addinin ya rasa kaninsa, Jeli Abubakar, yana da shekaru 64
- Jeli ya kasance kwamishinan harkokin cikin gida a Sokoto har zuwa mutuwarsa
Sultan na Sokoto, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya rasa kaninsa, Abdulkadir Jeli Abubakar III.
PM News ta ruwaito cewa Jeli ya mutu a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu yana da shekaru 64 a duniya.
Legit.ng ta tattaro cewa Jeli, wanda ya kasance kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Sokoto, ya mutu bayan yayi fama da rashin lafiya.
KU KARANTA KUMA: Daukar ma’aikata: Farin ciki fal yayinda wani gwamna ya amince da daukar matasa 4,000 aiki
Mai ba Gwamna Tambuwal shawara a kan labarai, Malam Muhammad Bello, ne ya tabbatar da mummunan labarin.
Ya ce tuni aka binne marigayin daidai da koyarwar addinin Musulunci, inda yace Gwamna Tambuwal ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga jihar da kasar baki daya.
Har zuwa mutuwarsa, Jeli Abubakar ya rike sarautar Dikkon Sokoto kuma ya mutu ya bar mata biyu, yara da yawa da jikoki.
Ya halarci makarantar firamare na Sultan da Nagarya College duk a jihar Sokoto kafin ya tafi makarantar koyon jarida a Ingila.
KU KARANTA KUMA: Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi
A wani labari na daban, mun ji cewa duk da dawowar annobar COVID-19 a kasar, gwamnatin tarayya ta ce bata tunanin sake rufe kasar.
Kwamitin Shugaban kasa kan korona a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, ta yi watsi da rahoton cewa tana shirin rufe kasar, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Willie Bassey, kakakin ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana rahoton sake rufe kasar a matsayin labarin karya. Ya ce irin wannan labarin karyan na iya haddasa fargaba mara ma’ana da tashin hankali a tsakanin mutane.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng