Daukar ma’aikata: Farin ciki fal yayinda wani gwamna ya amince da daukar matasa 4,000 aiki
- Gwamnatin jihar Niger ta sanar da sabon tsarin tsaro a jihar
- Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Abdulmalik Sarkin Daji, ya ce sabon tsarin zai yi aiki da matasa
- Daji ya yi bayanin dalilin da yasa aka dauki sabon tsarin tsaron
Gwamna Abubakar Sani Bello ya amince da daukar matasa 4,000 aiki a fadin jihar Niger.
Gwamnatin jihar ta sanar da cewa za a kwashi matasan aiki daga kananan hukumomi 25, jaridar The Guardian ta ruwaito.
A cewar kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Abdulmalik Sarkin Daji, za a dauki ma’aikatan ne don samar da yan sandan jiha.
KU KARANTA KUMA: Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi
Ya ce gwamnatin na fatan rage matsalolin tsaro da ke tunkarar jihar ta hanyar amfani da yan sandan jiha.
Kwamishinan ya ba hukumomin tsaro tabbacin samun tallafin gwamnati ta bangaren sama masu kayayyakin amfani da sauransu.
Ya kuma jinjinawa kwamishinan yan sandan jihar Niger, Adamu Usman, kan yadda yake tsaron jihar.
Daji ya bayyana cewa Shugaban yan sandan ya yi nasarar kare rayuka da dukiyoyin al’umman jihar da dan abunda ke hannunsa.
KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan batun sake rufe kasar
A gefe guda, ana jifan dakarun jami’an tsaron da gwamnoni suka kafa a jihohin Kudu maso yammacin Najeriya, WNSN, da laifin keta hakki da cin zarafin al’umma.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ana zargin sojojin Amotekun da hallaka Bayin Allah. Tuni kungiyoyi da lauyoyi masu kare hakkin Bil Adama suka fara yin kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo karshen aika-aikan da Amotekun su ke yi.
Rahoton yace lamarin Amotekun ya na nema ya zo da matsala musamman a jihar Oyo, inda dakarun suke rike bindigogi da sauran makamai masu hadari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng