Jami'an tsaro sun yi awon gaba da Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna cikin dare
- Gammayar jami'an tsaro sun kai sumame gidan Shaihi Dahiru Usman Bauchi na Jihar Kaduna sun kwashe masa almajirai
- Fatahu Umar Pandogori, shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye Kaduna ya tabbatar da afkuwar lamarin
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce nan bada dade wa ba za ta fitar da karin bayani game da lamarin
Jami'an tsaro a Jihar Kaduna sun shiga cikin gidan Shaihi Dahiru Bauchi sunyi awon gaba da dukkan aljamiran dake kwance a tsakar gidan a cewar rahotanni.
Fatahu Umar Pandogori, shugaban makarantun Dahiru Bauchi da ke Kaduna da kewaye kuma liman a masallacin Bye Pass na Kaduna ya tabbatarwa BBC faruwar lamarin.
"Misalin karfe 12 na dare Soji da 'Yan sanda da Road Safety da 'Yan Kastelea sun shigo gidan malaminmu Shehi, nan makaranta, suka kama almajirai suka yi awon gaba da su," in ji shugaban makarantar.
Ya ce bai san takamaiman dalilin da yasa aka kama almajiran ba, amma an sallami daliban makarantar tun bullar korona karo na farko, sai dai, a cewarsa, wadanda aka kama a yanzu din wadanda ke zaune ne a gidan Shaihi Dahiru ne ba wadanda suka taho daga wasu garuruwa bane.
"Ba zan iya bada takamaiman adadin almajiran da aka tafi da su ba, domin cikin dare ne aka zo aka tafi da su," ya ce.
A halin yanzu dai babu wani takamamen dalilin yin wannan kame duk da cewa a baya gwamnatin jihar ta taba kwace lasisin wata makaranta da ake zargi da saba dokokin dakile yaduwar ta korona.
A cikin shekarar 2020 da ta gabata, jihohi musamman na Arewa sun rika mayar da almajirai zuwa jihohinsu na ainihi kan zargin cewa suna yada cutar a tsakanin al'umma, wadda hakan ya janyo cece-kuce tsakanin wasu jihohin.
KU KARANTA: Matar aure ta bar mijinta don auren ɗan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'
Kazalika, gwamnan jihar na Kaduna a yan kwanakin nan ya gargadi al'ummar jihar cewa akwai yiwuwar sake dawo da dokar kulle idan ba a bin dokokin kiyayye yaduwar cutar da suka hada da saka takunkumi da bada tazara da sauransu.
Wannan gargadin ya yi dai-dai da na kwamitin yaki da annobar korona ta shugaban kasa, wato PTF, inda ta ce ya zama dole yan kasar su rika bin dokokin don gudun komawa gidan jiya duk da cewa daga bisani ta kawar da yiwuwar saka dokar.
Ya cigaba da cewa, sun yi kokarin tuntubar gwamnatin Kaduna a lokacin da abin ya faru, amma ba su samu sunyi magana da su ba.
BBC ta tuntubi gwamnatin Kaduna kan batun inda ta ce a halin yanzu ba za ta ce komai ba sai dai nan bada dadewa ba za ta fitar da karin bayani.
Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.
Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng