Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita daga dare zuwa safe, ta bayyana dalili

Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita daga dare zuwa safe, ta bayyana dalili

- Ayyukan yan bindiga a Benue ya zarce tunani a yanzu

- Domin yiwa tufkar hanci, gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe

- Gwamnatin ta sanar da cewa hakan ya fara aiki daga ranar Asabar, 13 ga watan Janairu

Majalisar tsaro ta jihar Benue ta sanya dokar kulle daga dare zuwa safe a Katsina Ala da karamar hukumar Ukum na yankin Sankera da ke jihar.

An sanya dokar ne don magance matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane da fashi da makami wanda ya yi yawa a yankunan.

Mataimakin gwamnan, Benson Abounu wanda yayi sanarwar a ranar Lahadi ya bayyana cewa dokar kullen zai fara aiki daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe a kullun.

Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita daga dare zuwa safe, ta bayyana dalili
Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita daga dare zuwa safe, ta bayyana dalili Hoto: @SamuelOrtom
Source: UGC

Dokar kullen ya fara aiki daga ranar Laraba, 13 ga watan Janairu, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dattawan Arewa: Babu wani dalili da zai sa Musulmai da Kiristoci yaki da juna

Mataimakin gwamnan ya kuma yi bayanin cewa majalisar ta yanke shawarar ci gaba da haramta amfani da babura a yankin da aka fi sani da Sankera har zuwa lokacin da za a sake duba lamarin tsaro a yankin.

“Zirga-zirgan marasa lafiya da masu ciki yana da matukar muhimmanci don haka za a bari suyi sha’aninsu a kan babur bayan an yi gagarumin bincike,” in ji Abounu.

Ya ce majalisar ta lura cewa masu tuka babur sun tashi daga yankunan da aka sanya haramcin zuwa garuruwan da ke makwabtaka inda suke haddasa fargaba.

Sannan ya bukaci hukumomin tsaro da su sanya idanu sosai a yankunan.

Ya kara da cewa hukuncin haramta amfani da babura a yankin Sankera na jihar biyo bayan hare-haren da aka kai kan mazauna Ukum da Katsina wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Yayinda yake jinjinawa ayyukan tsaro a yankin, ya ce haramcin ya sa an cimma nasara dari bisa dari.

Musamman yadda aka daina samun hare-hare da kashe kashe tun bayan sanya haramci kan babura a yan makonni da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Kukah: Jigon APC ya zargi JNI da kokarin hada rikicin addini, ya roki Buhari da Tambuwal su shiga lamarin

Abounu ya yi gargadin cewa duk wani mutum da aka kama yana take doka ko yana tuka babur wanda aka haramta a yankin, zai fuskanci hukunci mai tsauri.

A watan Disamba majalisar tsaro na jihar ta sanya haramci a kan babura a Katsina-Ala da karamar hukumar Ukum.

Sai dai an bari masu adaidaita da sauran ababen hawa suna ta sha’aninsu a kananan hukumomin biyu.

Majalisar ta kuma wajabta cewa baya ga tashar karbar haraji da ke kan gada a Katsina-Ala, babu wani tasha da aka yarje ma yayi aiki a cikin karamar hukumar.

A wani labarin kuma, har yanzu, harkokin tsaro sai kara tabarbarewa suke yi, don da safiyar Alhamis, 14 ga watan Janairu wasu mutane, da ake zargin 'yan fashi ne suka kashe wani Mustapha Abubakar a jihar Kano.

Dan uwan Abubakar ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yace sun harbi dan uwansa ne da safiyar Alhamis.

Kamar yadda yace, Abubakar yana hanyar komawarsa gida daga masallaci mummunan lamarin ya auku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel