Sadiya Umar Farouk ta ce Gwamnati za ta yi wa matan karkara rabon N20000

Sadiya Umar Farouk ta ce Gwamnati za ta yi wa matan karkara rabon N20000

- Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa mata masu karamin karfi a Najeriya

- Ministar bada tallafi tace mata 160, 000 ne za su ci moriyar wannan tsari

- Sadiya Farouk tace mata 6800 aka zaba za a rabawa kudin a jihar Katsina

Akalla mata 6, 800 daga kauyuka da karkarorin jihar Katsina za su amfana da tsarin da gwamnatin tarayya ta shigo da shi na tallafawa marasa galihu.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnatin tarayya za ta raba kudi domin bunkasa rayuwar marasa hali.

Ministar bada tallafi da agajin gaggawa da cigaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta bayyana wannan da ta ke jawabi a garin Katsina.

Da take jawabi a ranar Laraba, 13 ga watan Junairu, 2021, Ministar ta ce mata sama da 160, 000 za su amfana da wannan tsari a fadin jihohin Najeriya.

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya ba dalibin jami'a da ke jinya tallafin N10m

Sadiya Umar Farouk ta shaidawa ‘yan jarida cewa kowace mace da aka zaba za ta samu N20, 000.

Wannan tsari ya na cikin shirin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da shi domin taimakawa marasa karfi a lokacin da ake fama da COVID-19.

Ministar ta yi kira ga wadanda aka zaba domin a ba wannan kudi su yi amfani da abin da za a ba su wajen habaka kudin shigarsu da tanadar kayan abinci.

Sadiya Umar Farouk ta kuma yi kira ga wadannan mata da su ka yi dace, suyi amfani da kudin da gwamnati za ta ba su wajen inganta halin rayuwar da su ke ci.

KU KARANTA: Musulami sun yi wa Mathew Kukah raddi, sun zarge shi da ‘munafunci'

Sadiya Umar Farouk ta ce Gwamnati za ta yi wa matan karkara rabon N20000
Sadiya Umar Farouk Hoto: Twitter Daga: @Sadiya_farouq
Asali: Twitter

Mataimakin gwamna, QS Mannir Yakubu wanda ya wakilci gwamnan Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya gode da kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi.

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta rabawa Jihohi 34 biliyoyin kudi inda aka ga Sokoto ce kan gaba yayin da gwamna Aminu Waziru Tambuwal ya samu N6.6bn.

Gwamnatin Tarayya ta ba wasu Jihohin N123bn ne a karkashin shirin STFTAS da aka fito da shi.

Ministar tattali da kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar ta hannun Hassan Dodo a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel