Zulum ya bawa dalibin jami'a tallafin N10m domin yi masa aikin koda

Zulum ya bawa dalibin jami'a tallafin N10m domin yi masa aikin koda

- Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno, ya amince da bayar da tallafin miliyan goma domin ceto rayuwar wani dalibi

- Dalibin mai suna Mbahi Sarki Suleiman da iyayensa sun nemi taimakon gwamna a wani shirin gidan Talabijin

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Talata ya saka hannu a biya miliyan ₦10 don ceto rayuwar Mbahi Sarki Suleiman,wani matashin ɗalibi mai karantar kimiyyar yanayi (Geography) a jami'ar Maiduguri.

Zulum ya bawa dalibin tallafin ne sakamakon matsananciyar jinya har ta kai jallin yana buƙatar dashen ƙoda.

Ɗalibin ɗan asalin ƙauyen Yara daga ƙaramar hukumar Hawul dake kudancin Borno.

Tallafin ya biyo bayan rokon da ɗalibin da mahaifiyarsa suka sha yi a shirin "Brekete Family"; wani shirin gidan rediyo da talabijin da ke karbar korafi da sauran harkoki akan hakkin jama'a da ke Abuja.

Ana gudanar da shirin a karkashin jagorancin wani lauya mai suna Ahmed Isa wanda ake yiwa take da "Ordinary President" wanda ya yi roko ga Gwamna Zulum akan ya ce ci Bitrus.

Iyalan matashin sun buƙaci miliyan ₦9 don yi masa dashen ƙoda, a cewarsu, akwai wanda zai bayar da ƙodarsa a dasawa ɗan uwansu.

Zulum ya bawa dalibin jami'a tallafin N10m domin yi masa aikin koda
Zulum ya bawa dalibin jami'a tallafin N10m domin yi masa aikin koda @ProfZulum
Asali: Twitter

A ranar Talata, 12 ga watan Junairu,masu yaɗa labaran gwamnan suka jawo hankalin Gwamna Zulum inda anan take ya bada Umarnin sakin miliyancn ₦10 don yiwa matashin aiki.

Gwamna Zulum ya ƙara miliyan ₦1 akan adadin saboda tsaro duk da iyalan mamacin miliyan ₦9 suka buƙata.

Washegari, ranar Laraba, Mahaifiyar matashin mai suna Saratu Sarki Bitrus ta dawo shirin da ɗanta, inda ta tabbatar da cewa sun samu miliyan ₦10 daga gwamna Zulum,kuma tuni suka biya kuɗin a wani asibiti da ke Abuja, kuma ana sa ran cikin satin nan za'ayi aikin.

Da yake magana cikin kukan Farinciki, majinyacin Mbahi ya ce shine ya ga saƙon shigowar kuɗin cikin wayar Mahaifiyarsa.

Ina ganin shigowar kuɗin farinciki ya kamani, nan take na fashe da kukan farinciki.

Daga baya, wani hadimin gwamnan ya kira domin jin ko mun samu saƙon gwamnan inda muka tabbatar masa da hakan.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, sun yi alhini tare da juyayin mutuwar wata mai kusanci da su, Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman.

Marigayiya Nafisatu mata ce wurin Laftanar Kanal IG Usman, dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.

A cikin sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga gidan sarautar Adamawa, gwamnatin jiha da kuma jama'ar jihar baki daya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel