Gwamnatin Tarayya ta ba wasu Jihohi N123bn a karkashin shirin STFTAS

Gwamnatin Tarayya ta ba wasu Jihohi N123bn a karkashin shirin STFTAS

- Gwamnatin Muhammadu Buhari ta sake raba wasu kason kudi ga jihohi

- An fitar da wannan kudi ne karkashin tsarin STFTAS da aka shigo da shi

- Gwamnati ta kawo shirin ne domin tabbatar da gaskiya wajen kashe kudi

Jaridar Daily Trust ta ce an rabawa jihohin Naira biliyan 123.48 ($324.6m) ne saboda gaskiya da ke-ke-da-ke-ke suka nuna wajen batar da kudin al’umma.

Ministar tattali da kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar ta hannun Hassan Dodo a ranar Laraba a Abuja.

Darektan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tarayyar, Hassan Dodo ya ce an yi la’akari da sakamakon kokarin da jihohin sukayi wajen raba kudin.

Ofishin mai binciken kudi na kasa watau OAuGF ne ya gudanar da wannan aiki wanda ya samu shaidar sashen PCU na ma’aikatar tattali da kasafin kudi.

KU KARANTA: Hadimin Ganduje ya bayyana wadanda su ke juya akalar Kano

Kamar yadda Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana, kason ya kunshi N91.048b da aka rabawa jihohi 32 saboda kokarin da su ka yi wajen tattalin arziki.

Jihar Sokoto wanda ta tashi da Naira biliyan 6.612 ta zo ta farko cikin wadanda suka samu wannan kudi. Kano ce ta karshe a jerin da Naira biliyan 1.710.

Jihohin Bayelsa, Imo, Ribas da Zamfara ba su samu komai daga cikin wannan kaso ba saboda gazawarsu na cika sharudan da aka gindaya masu a 2019.

Daga cikin sharudan da gwamnatin tarayya ta ba jihohin shi ne wallafa kasafin kudin jiha da binciken kudin da gwamnati ta batar daga lokaci zuwa lokaci.

KU KARANTA: Minista ya ce Matasa za su samu abin dogaro a karkashin ESPWP

Gwamnatin Tarayya ta ba wasu Jihohi N123bn a karkashin shirin STFTAS
Zainab Ahmed Shamsuna Hoto: Twitter Daga: @Shamsuna
Asali: Twitter

Ministar tace sun kuma raba Naira biliyan 32.3 domin yaki da annobar cutar COVID-19, a nan ma Anambra da Zamfara ne kawai ba su iya samun kaso a rabon ba.

Kungiyoyin SSANU da NASU sun bijirewa sharudan COVID-19, sun gudanar da zanga-zanga domin nunawa gwamnatin tarayya fushi da rashin jin dadinsu.

Idan za ku tuna kungiyoyin ma'aikatan jami’an sun taso shugaban kasa Muhammadu Buhari gaba, sun bukaci ya tsige Ministoci Adamu Adamu da Chris Ngige.

Bayan an samu an shawo kan kungiyar ASUU, gwamnati za ta fara fama da SSANU da NASU.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel