Matsi ya sa wasu direbobi bude tasha mai suna Tashar Buhari

Matsi ya sa wasu direbobi bude tasha mai suna Tashar Buhari

- Matsi ya sanya wasu mazauna a wani yankin jihar Kano kirkirar wata tashar mota dan saukake zirga-zirga

- Tashar da suka kirkira sun sanya mata suna tashar Buhari sakamakon matsanancin tattalin arzikin da ake fuskanta a mulkinsa

- Tasha ce da mutum zai iya hawa mota a kan kudi kasa da Naira 50

Jerin gwano kanana da matsakaitan motoci, dauke da fasinjoji zuwa yankunan Kurna, Rijiyar Lemo da Bachirawa a wata tasha na wucin gadi da ake kira Tashar Buhari (Wurin Motar Buhari) ya zama shahararren wuri a jihar Kano.

Direbobin kananan motoci ne suka sanya wurin kaurin suna a jihar ta Kano.

Tashar motar, wanda aka fi sani da Tashar Buhari, ya sami sunanta ne saboda halin matsin tattalin arziki da kasar nan ke ciki a wannan gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Ahmad Lawan ya bai wa gwamnati shawarin ta daina bijiro da uzuri

Sabuwar Tashar Buhari a jihar Kano
Sabuwar Tashar Buhari a jihar Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Direbobin ne suka shaidawa jaridar Chronicle a yayin wata hira da suka yi da wasu ma'aika a cikin tashar.

Tashar aa wucin gadi ta wanzu ne kimanin shekaru hudu da suka gabata don magance kalubalen mutanen da ba za su iya biyan kuɗin hawa a daidaita sahu ko tasi ba tare da babu wata hanyar zirga-zirga mallakin gwamnatin jihar, in ji Chronicle.

Kafin kafuwar tashar na wucin gadi, mutane da yawa kan taka zuwa gida idan ba za su iya biyan kudin safarar daga harkokin yau da kullum a kasuwanni ba.

Amma da tafuwar tashar, matafiya, akasarinsu tsofaffi maza da samari matasa wadanda ke gudanar da kananan sana'o'i, yanzu haka za su iya hawa manyan motoci zuwa da dawowa daga inda za su tafi da dan abin da bai kai N40 ba ko ma kyauta.

Direbobin manyan motocin kuma sun ce baya ga wahalar da ta sha gabanin kafa tsahar; Matsalar yawan jama'a a yankin Kurna (wanda ake kira da sunan Chinatown saboda yawan jama'a) ya kuma tilasta wa wasu mutane shiga motocin.

Wani jagoran direbobin manyan motocin, Malam Mani, ya ce sun yanke shawarar kafa tashar Buharin ne domin saukaka wahalhalu da masu karamin karfi ke fuskanta yayin da suke kokarin aikin cin abincin su na yau da kullun.

“Tare da zuwan Tashar Buhari, mutane sun sami sauki don zuwa wurare daban-daban da za su je a kan lokaci, tare da araha da saukake wahala. Mutane da yawa ba su iya biyan N100 don jigilar kaya.

"Da yawa ba su da shi, su kan yi tafiya a kafa daga wannan tashar zuwa yankin Kurna. Amma idan kunzo wannan wuri, koma dai menene, zaku dawo gida. Idan ba ku da kuɗi, za mu roƙi direbobin su taimake ku.

“Ba mu da direbobi na dindindin wadanda koyaushe suna nan don daukar fasinjoji. Bayan (direbobin manyan motoci) sun gama aikinsu sai su zo wannan wurin don ɗaukar mutane.

"Muna karbar N40 a kowane mutum kuma suna daukar fasinjoji tsakanin 15 zuwa 20,” ya kara da cewa.

Mani ya ce ba a cajin direbobin manyan motoci wasu kudade tunda suna taimaka wa mutane su dawo gida cikin sauki.

KU KARANTA: IPPIS: SSANU, NASU suna zanga-zangar lumana

Wani fasinja, Malam Lawan, ya ce dole ne ya taka a duk lokacin da ya kasa samun kudin zuwa kasuwa ko komawa gida. “Amma da zuwan Tashar Buhari, yanzu zan iya komawa gida da N30 kawai."

Tashar Buhari ta zama abin share hawaye ga marasa karfi a wannan yaki na jihar Kano.

Masu hawa motocin da kuma direbobin sun bayyana cewa, matsi da aka shiga na tattalin arziki da ya jawo tsadar abubuwan more rayuwa a kasar shi ya jawo nemawa mutane mafita ta fanninn sufuri a yankin.

A wani labarin daban, Wani dan majalisa, mai wakiltar Bodinga-Dange, a mazabar tarayya ta Shuni-Tureta, Dr. Balarabe Kakale ya ware naira miliyan 200 domin karfafawa Almajiri da kananan ‘yan kasuwa a mazabar sa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan rarraba motoci tara, babura 33, kekunan dinki 60, injunan nika 40 da sauransu ga wadanda suka fara cin gajiyar shirin, ya ce an yi hakan ne domin a hana Almajirai yin bara. Y

a kara da cewa yana harin tallafawa almajirai 1000 ne a wannan shekarar kadai, ya kara da cewa shirin zai ci gaba ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.