Tsohon kwamishinan Ganduje: Duk da ilimin gwamna, wasu tantirai kuma jahilai ke sarrafa akalar gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan Ganduje: Duk da ilimin gwamna, wasu tantirai kuma jahilai ke sarrafa akalar gwamnatin Kano

- Injiniya Mu'azu Magaji, tsohon kwamishinan aiyuka na jihar Kano, ya cigaba da tayar da kura a shafinsa na dandalin sada zumunta

- Ganduje ya sauke Injiniya Magaji daga mukamin kwamishina a shekarar 2020 sakamakon wallafa wani rubutu dangane da mutuwar Abba Kyari

- Ana takun saka tsakanin tsohon kwamishina da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu'azu Magaji, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook cewa tantirai, marasa ɗa'a da tarbiyya ke jan akalar jihar Kano.

Ya ce wasu tsageru wanda basu da ilimin addini da na zamani sune ke jan ragamar siyasar jihar Kano.

Sai dai maganar tasa ta yamutsa hazo inda ta haifar da jayayya tare da haifar da cece-kuce a tsakanin jama'a, musamman 'yan siyasa.

KARANTA: Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta

Ya rubuta cewa; "jahilci ba ado ba ne, babbar illa ce ga rayuwa da cigaba da dorewar zaman lafiyar al'umma.

Jihar Kano yana da Gwamna mai Phd da ilmin addini amma duk da haka wasu tantirai; babu arabi ba boko, sune ke jan ragamar al'lamurran mu na siyasa da rayuwa."

Tsohon kwamishinan Ganduje: Duk da ilimin gwamna, wasu tantirai kuma jahilai ke sarrafa akalar gwamnatin Kano
Tsohon kwamishinan Ganduje: Duk da ilimin gwamna, wasu tantirai kuma jahilai ke sarrafa akalar gwamnatin Kano
Source: Facebook

Sai dai mabiya shafinsa sun maida raddi gami zafafan martani.

KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta karrama marigayi AIG Bishi da faretin bankwana, an binne gawarsa cikin hawaye

Ganduje ya sauke Injiniya Magaji daga mukamin kwamishina bayan ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebool bayan muuwar tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, marigay Abba Kyari.

Daga baya Ganduje ya nada Injiniya Magaji a matsayin mai kula da aikin janyo bututun man fetur zuwa Kano, kamar yadda Freedom Radio ta rawaito.

Ba'a ga maciji a tsakanin tsohon kwamishinan da shugaban jam'iyyar APC a Jihar Kano, Abdullahi Abbas.

Hatta a ranar Ltinin, 11 ga watan Janairu, sai da Injiniya Magaji ya bukaci Abdullahi Abbas ya je a yi masa gwajin amfani da miyagun kwayoyi, lamarin da ya haddasa muhawara mai zafi a shafinsa na Facebook.

Sai dai, har yanzu hedikwatar jam'iyyar APC a jihar Kano ba ta ce komai dangane da sakonni masu tayar da kura da Dan Sarauniya ke wallafa a dandalin sada zumunta ba.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan kwangilar gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi da kuma daga Kano zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Minsitan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya saka hannu akan kwangilar da aka bawa wani kamfani mai suna Mota-Engil Group.

Kamfanin Mota-Engil Group ya dauki gina jami'a kafin ya kammala aikin a matsayin tukuicin aikin da zai yi a Nigeria.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel