Wasu kungiyoyin Jami’a sun taso Buhari gaba, sun bukaci ya tsige Adamu da Ngige a dalilin EAA

Wasu kungiyoyin Jami’a sun taso Buhari gaba, sun bukaci ya tsige Adamu da Ngige a dalilin EAA

- ‘Ya ‘yan kungiyar NASU da SSANU sun fara zanga-zanga a Najeriya

- Ma’aikatan suna bore ne kan matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka

- NASU da SSANU sun ce sai an biya masu bukatu za a iya bude jami’a

Kungiyar NASU da SSANU na ma’aikatan jami’a wadanda ba su shiga aji sun fara zanga-zanga a wasu jami’o’in da ke fadin kasar nan.

Jaridar Vanguard ta ce ma’aikatan suna bore ne saboda wasu matakai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka a kan jami’o’in kasar.

Rahoton ya ce daga cikin dalilan da su ka jawo wannan zanga-zanga shi ne shigo da tsarin biyan albashi ta manhajar IPPIS da gwamnatin tarayya ta yi.

Bayan haka ‘ya ‘yan kungiyar NASU da SSANU sun bukaci gwamnatin tarayya ta duba yadda aka yi kason alawus din EAA da za a biya ma’aikatan jami’a.

KU KARANTA: An soki yadda Buhari yake rabon mukamai da karbo aron kudi a hannun China

Bugu da kari, ma’aikatan sun ce ba za a bude jami’o’in gwamnati ba har sai an biya su bashin da suke bi na karin albashi da aka yi a 2019.

‘Yan kungiyar NASU da SSANU da suka fara zanga-zanga a makon nan sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami wasu Ministocinsa.

Wadannan Ministoci sune Malam Adamu Adamu da Dr. Chris Ngige wadanda suke rike da ma’aikatar ilmi da na kwadago na tarayya.

Laifin Ministocin shi ne amincewa da bukatun kungiyar ASUU na biyan Naira biliyan 40 a matsayin alawus din karin aiki, wanda su aka ware su a gefe.

KU KARANTA:Coronavirus ta kai intaha, ana gab da cike gadajen asibiti da masu jinya

Wasu kungiyoyin Jami’a sun taso Buhari gaba, sun bukaci ya tsige Adamu da Ngige a dalilin EAA
Shugaban SSANU Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

An gudanar da wannan zanga-zanga jiya a manyan garuruwa da su ka hada da Legas, Ibadan, Kalaba da birnin tarayya Abuja duk da ana fama da COVID-19.

A baya kun ji cewa dawowar cutar Coronavirus ta sa Gwamnati ta na shirin fasa komawa karatu.

Gwamnati ta zauna domin duba lokacin da dalibai za su koma shiga aji bayan an dakatar da karatu saboda annobar COVID-19 da ta addabi kasashen Duniya.

Ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu yace su na duba yiwuwar sake bude makarantu a ranar 18 ga watan Junairu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng