Ogbonnaya Onu: Za a koyawa mutane 13, 000 da ke zaman kshe wando aikin yi
- Ministan kimiyya da fasaha yace mutane za su samu abin yi ta tsarin ESPWP
- Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin tarayya za ta koyawa mutane 13, 000 aiki
- Ministan ya roki kamfanoni da su dauki matasan aiki bayan sun samu horo
Ministan kimiyya da fasaha na kasa, Dr. Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin tarayya za ta inganta rayuwar matasa 13, 000 a Najeriya.
Jaridar Vanguard ta rahoto Ministan yana cewa za a dauki wadannan matasa aiki a bangarori uku na gwamnati da ake da su.
Mai girma Ministan ya bayyana haka ne a garin Abakaliki, jihar Ebonyi, wajen kaddamar da shirin daukar aikin ESPWP da gwamnati za ta yi.
Ogbonnaya Onu ya ce an kawo wannan shiri ne domin inganta ayyukan kananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya a kasar.
KU KARANTA: Mun kashe N120bn a kan COVID-19 - FG
Dr. Onu ya cigaba da cewa amfanin wannan shiri da gwamnatin APC ta dauko shi ne a tabbatar da dorewar ayyukan da gwamnatin ta ke yi.
“A kowace karamar hukuma aikin da za ayi ya sha ban-bam, amma makusudin shi ne tabbatar ana yin ayyukan gwamnati da kyau, kuma suna dorewa.” Inji Onu.
Ministan a jawabinsa, ya yi kira ga wadanda za su amfana da wannan shiri su nuna jajircewarsu da nufin su samu abin dogaro.
Bayan haka, Onu ya roki ‘yan kasuwa masu zaman kansu, su dauki matasan da za horas aiki bayan sun samu kwarewa da sanin makaman aiki.
KU KARANTA: Sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya zai fara aiki
A jawabin da Ministan ya gabatar gaban jami’an gwamnatin Ebonyi da NDE, ya ce gwamnatin tarayya za ta sa ido a game da yadda ake dabbaka shirin.
A makon jiya kun ji wani labari mai firgici cewa bayan shekaru da dauke wasu yara daga Kano, an same su a wasu gidajen marayu da ke yankin Kudu.
Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ce ta gano kananan yaran da aka sace ne bayan kwamitin da aka kafa domin wannan aiki ya binciki wasu gidajen marayu.
Kwamishinan labarai, ya ce an dauke wadannan yaran an kai su kasar Ibo ne daga jihar Kano.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng