Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano

Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano

- Jama'a sun yamutsa gashin baki a kan hotunan wasu ma'aurata da aka zarga da yin auren zobe a jihar Kano

- Ana ganin wannan shiri sam bai dace da koyarwar addinin musulunci ba saboda ganinsu da aka yi a gaban alkali

- Sai dai kuma sabanin rade-radin, an daura auren ne bisa sunnah kuma a masallaci

Hotunan wasu ma’aurata yan jihar Kano da aka zarga da yin auren zobe ya janyo cece-kuce a tsakanin mutane. Wasu da dama na ganin hakan bai dace da al’adar Mallam Bahaushe da koyarwar addinin Musulunci ba.

Wakilin Legit.ng, Sani Hamza Funtua ya zanta da ainahin mai hoton da ya dauki dukka shagulgulan bikin, Musa Adam Kanti don jin yadda gaskiyar abun yake.

A nan ne ya gano cewa ainahin labarin da ake ta yayatawa duk kanzon kurege ne domin Adam Kanti ya yi bayani dalla-dalla.

Ya bayyana cewa tun a watan Nuwamban 2020 aka daura auren masoyan wanda dukkansu yan asalin jihar Kano ne. Amma sai aka samu tsaiko sakamakon jiran bizan amaryar saboda mijin a kasar Faransa yake da zama da aiki.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano
Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano Hoto: Abdulwahab Mustapha Labo
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari

Wannan dalili ne yasa suka je ma’aikatar cikin gida na Kano, sashen halasta aure domin yin rijistar aure a dokance.

Hakan ne zai bai wa ita matar damar samun biza zuwa Faransa. Kuma mallam Dr. Bashir Kano shine ya daura auren sannan ya ba su takardar shaidar aure.

Ga yadda hirar tasu ta kasance:

"Tambaya: Akwai wani aure da aka daura a hukumar kulla yarjejeniyar aure ta Kano mutane na cece-Kuce cewa auren zobe aka yi.

"Amsa: Eh aure aka yi bisa sunnah kuma duk wani abu da kake tunani ana yi kan aure anyi, kuma a masallaci aka daura kuma duk bukukuwan auren ni na dauke su.

“Wannan ba wai wani abu ake bukata ba illa tafiya da Za su yi. Dukkansu yan Najeriya ne Amma shi mijin ba a nan yake da zama ba, sai suka hadu suka yi aure shine ana nema mata biza da za ta je chan ta zauna shine aka je kotu.

“Akwai wasu ma da suka ce wai kila ba Musulmai bane.”

Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano
Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano Hoto: Abdulwahab Mustapha Labo
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Me suke so suyi? CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto

A wani labari, Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya samu karuwar 'yan biyu da amaryarsa ta haifa masa.

Hotuna a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun nuna yadda gwamnan ke farin cikin samun karuwar.

Wannan na zuwa bayan dawowan gwamnan daga kasar Amurka inda ya je duba yaransa dake karatu a can.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel