Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a

Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a

- Allah ya amshi ran wani matashi da ya yi hasashen mutuwarsa

- Matashin mai suna Adam Hamza Soye ya fada ma abokinsa cewa ya ji a jikinsa karshensa ya zo

- Mutuwar tasa ya girgiza jama'a da dama tare da jefa su cikin halin juyayi

Rasuwar wani matashi da ya yi hasashen mutuwarsa ya sanya girgiza jama’a musamman abokansa da masu kusanci da shi.

Matashin mai suna Adam Hamza Soye kafin mutuwarsa, ya yi hira da wani abokinsa a kafar sada zumuntar WhatsApp inda ya sanar da abokin nasa cewa shi yana ji a jikinsa kamar mutuwa zai yi.

Sai dai abokin nasa ya kwabe shi a kan ya daina fadin haka domin duk mai rai mamaci ne. Allah cikin ikonsa kuwa sai ya dauki ran wannan bawa nasa.

Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a
Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a Hoto: Abdulwahhab Nasir Isah
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano

Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Mamacin ya ce: “Naji kaman mutuwa xanyi."

Sai abokin nasa yace: "Kada ka fara dan Allah, kowa Zee mutu, amma ba yanzu ba.”

Sai mamacin ya kara cewa: “Ba haka bane, dawo dani gida akayi pah.”

Sai shi kuma abokin nasa ya kara cewa: “Ehh dai nkm kadena wannan mgn dan Allah.”

Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a
Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a
Source: UGC

Wani mai amfani da shafin Facebook, Abdulwahhab Nasir Isah ne ya wallafa labarin mutuwar tasa tare da mika ta’aziyya ga iyaye da yan uwan mamatan.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari

“Cikin kad'uwa da juyayi nake isar da saqon ta'aziyyah a madadin ni, mahaifina da sauran iyalan gidan mu.

"Zuwa ga shugaban Hukumar wasanni na jihar Gombe, Mallam Hamza Adamu Soye bisa rasuwar d'ansa matashi mai suna Adamu Soye Hamza."

"Saqon ta'aziyyah na zuwa ga ilahirin d'aliban jami'ah mallakar jihar Gombe (GSU) musamman na tsangayar kimiyyah a bangaren koyar da lissafi (Mathematics Department).

"Adam Hamza Soye kafin rasuwar sa yakasance lafiyayyen matashi mai hazaqa, ya bar duniya yana karantar ilimin kimiyyar na'ura mai qwaqwalwa (Computer Science) ajin qarshe a jami'ar jihar Gombe.

“Janazar sa zata kasance anjima bayan idar da sallar azahar da misalin qarfe 01:00pm, a masallacin jumu'ah na babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake nan Gombe.

“Muna addu'ah dafatan ubangiji Allah ya gafarta masa, ya karbi tubansa, yasa aljannar Firdausi ta kasance makoma a gareshi. Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.”

A wani laarin, tsohon dan majalisar dokokin Jihar Kaduna Abdullahi Jumare ya rasu bayan fama da gajeriyar jinya.

Marigayin ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin Kaduna daga shekarar 2012-2015.

An yi jana'izar sa a karamar hukumar Makarfi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel