Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari

Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari

Ana ci gaba da tattauna yadda tseren shugabancin 2023 zai kasance, koda dai masana harkokin siyasa na ganin cewa ya yi wuri da yawa da za a mayar da hankali ga inda shugaban kasa na gaba zai fito.

Ga dukkan alamu, Jam’iyyar APC mai mulki na iya mika tikitin takarar Shugaban kasarta ga yankin kudu bayan kammala wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hakan ya sa kallo ya koma yankin kudu maso yamma da kudu maso gabas.

Manyan mambobin jam’iyyar mai mulki a ranar Talata, 15 ga watan Disamba suka kaddamar da kamfen din Shugaban kasa na Bola Tinubu mai taken: "The South-West Agenda (SWAGA)".

Koda dai ana ta rade radin cewa wasu manyan mutane da suka hada da Tinubu da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti suna hararar babban kujeran, babu wani jawabi a hukumance daga shugabannin biyu wanda ya tabbatar da hakan.

Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari
Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari Hoto: @ProfOsinbajo @Kfayemi, @AsiwajuTinubu
Source: Twitter

A halin da ake ciki, akwai zazzafan muhawarar cewa tunda Shugaban kasa mai ci ya fito daga arewa ne, ya kamata a mika mulkin zuwa kudu, inda kudu maso yamma da kudu maso gabas za su baje kwanjinsu.

KU KARANTA KUMA: Yadda hadiman Buhari suka bata masa suna, suka mayar da Nigeria abar dari, Dan majalisa ya bayyana

Yayinda ake ci gaba da zanta yadda tseren zai kasance a 2023, Legit.ng ta lissafo wasu mutane hudu da ake ganin za su iya gadar Buhari idan APC ko PDP suka yanke shawarar mika tikitinsu ga kudu maso yamma.

1. Bola Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Lagas kuma babban jigon APC, Tinubu yana hararar babban kujeran kasar idan wa’adin mulkin Shugaban kasa mai ci ya kare.

Koda dai tsohon gwamnan bai fitar da sanarwa a hukumance don tabbatar da hakan ba, bai fito ya yi watsi da lamarin da ke kewaye da kudirinsa na 2023 ba.

Ana ganin Tinubu zai samu mabiya sosai duba ga yadda makusantansa da masu masa biyayya ke fafutuka a kan zaben 2023.

Tsohon gwamnan ya kasance babban jigo a jam’iyyun siyasan da suka hade har suka gina APC a 2014.

2. Kayode Fayemi

Gwamnan Ekiti ma ana ganin yana hararar babban kujeran kamar ubangidansa Tinubu.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Fayemi ya yi aiki a matsayin ministan ma’adinai.

Ana sanya ran zai kuma kasance kan gaba a tattaunawar wannan shekarar, yayinda jam’iyyar mai mulki reshen jihar Ekiti ta fara fafutuka a kan kudirinsa.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da sabbin nade-nade

3. Yemi Osinbajo

Babu mamaki Najeriya bata taba samun mataimakin Shugaban kasa mai biyayya kamar Farfesan bangaren shari’a, Yemi Osinbajo ba.

Ana matukar ganin mutuncin Osinbajo wanda ya kasance fasto a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), a bangaren siyasar kasar saboda yadda yake tafiyar da lamuransa.

Ya yi aiki a matsayin kwamishinan shari’a na jihar Lagas karkashin Tinubu.

Saboda tarin kwarewarsa, ya samu gagarumin goyon baya na zama dan takarar mataimakin Shugaban kasa na Shugaba Buhari a 2015.

Yayinda mulkin Buhari ke zuwa karshe, an sako mataimakin Shugaban kasar cikin jerin yan siyasan kudu maso yamma da za su karbi shugabanci daga hannun Shugaban kasar.

A 2020, wata kungiya ta bukaci yan Najeriya da su marawa Osinbajo da gwamnan Borno, Babagana Zulum baya a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa.

4. Peter Ayo Fayose

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Ekiti kuma jigon jam’iyyar PDP ma ya samu goyon bayan neman wannan kujera ta Shugaban kasa.

A 2019, fostan neman zaben tsohon gwamnan ya karade unguwanni sannan aka yi wa motoci ado da hotunansa inda aka rubuta ‘sadu da Shugaban kasarku na gaba a 2019’.

Ana tsammanin Fayose zai yi yunkurin neman kujerar gabannin 2023, koda dai ba a jam’iyya mai mulki ba.

A wani labarin, wata kungiyar magoya bayan shugabancin Yahaya Bello mai suna PYB FRONTIERS ta yi kira ga mutanen Najeriya da su marawa gwamnan baya domin tabbatar da ganin cewa ya gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar, Hans Mohammed a wani jawabi ya ce kungiyar ta fara tattaunawa don tabbatar da ganin gwamnan ya samu tikitin APC, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya bayyana cewa gwamnan ya nuna bajinta a bangarorin tsaro, ilimi mai inganci, fannin lafiya musamman a lokacin annobar korona.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel