INEC: Mu na shirin kawo fasahohin zamani da za su takaita magudi a zabe

INEC: Mu na shirin kawo fasahohin zamani da za su takaita magudi a zabe

- Hukumar INEC ta shirya wani taro domin karawa juna sani a Jihar Nasarawa jiya

- Za a shigo da wasu dabarun zamani da zasu taimaka wajen inganta nagartar zabe

- Wani jami’in hukumar yace suna ta kokarin ganin yadda za a gyara harkar zaben

Vangard ta ce a ranar Talata, 12 ga watan Junairu, 2020, INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, ta ce tana sake duba fasahohin da ake amfani da su.

Hukumar INEC ta bayyana cewa tana yin wannan aiki ne da nufin kawo sababbin kirkire-kirkire da su inganta sha’anin zabe nan da shekarar 2023.

Darektan da ke kula da wayar da kan masu zabe da yada labarai, Nick Dazang, ya bayyana haka wajen wani taron karawa juna sani a Keffi, jihar Nasarawa.

Mista Nick Dazang ya ce hukumar zaben mai zaman kanta, ta gudanar da wannan taro ne domin a duba yadda ake bi wajen shirya zabe a Najeriya.

KU KARANTA: Alkawuran da ake jiran Shugaban kasa Buhari ya cika nan da 2023

Da yake magana da ‘yan jarida bayan taron, Mista Dazang ya ce tun a 2004 aka fara maganar shirya zabe ta hanyar na’urorin zamani a kasar nan.

“Bayan nan, sai a shekarar 2010, hukumar ta shigo da na’urorin tantance masu kada kuri’a, aka yi amfani da na’urorin a zaben 2011.” Inji Nick Dazang.

Jami’in ya kara da cewa: “Amma hukuma tana duba wannan tsari, da nufin a inganta shi domin a gyara yadda za ayi zaben 2023.”

“INEC tana so ta shigo da sababbin fasahohi da za su taimaka wajen gyara sha’anin zabe. Saboda haka, hukumar tana aiki a kan wannan.”

KU KARANTA: Za ayi maganin zaman banza ta horas da Matasa - Minista

INEC: Mu na shirin kawo fasahohin zamani da za su takaita magudi a zabe
Buhari Shugaban INEC Hoto: www.okay.ng
Asali: UGC

Wajen yin hakan, Dazang ya ce za a duba maganar na’urar ‘Card Reader’, a kawo wata fasahar da za ta bada dama ayi zabe da na’urorin zamani a 2023.

Jaridar ta ce gidauniyar nan ta Westminster Foundation for Democracy (WFD) ta shirya wannan taro.

A shekaran jiya ne kuma sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya yi magana game da wadanda za a ba tutar takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya ce gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, da tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara, za su bar APC, su sake dawowa PDP.

Sannan PDP ta ce ita ta lashe zaben Shugaban kasa a 2019, amma INEC ta yi mata coge.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel