Tsaro, tattalin arziki da aikin da ke gaban Buhari zuwa lokacin da zai bar ofis

Tsaro, tattalin arziki da aikin da ke gaban Buhari zuwa lokacin da zai bar ofis

- A shekarar 2015 ne Janar Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zaben Najeriya a jam’iyyar adawa wanda hakan ya ba shi damar zama shugaban kasa

- Muhammadu Buhari ya yi wa al’umma alkawuran tarin abubuwan da zai yi idan ya samu mulki. Shekaru kusan shida kenan da shugaban kasar ya shiga ofis

Jaridar The Guardian ta tattaro ragowar alkawuran da ake sa ran shugaban Najeriyar zai cika kafin ya bar mullki a 2023.

1. Tsaro

Kawo karshen rashin tsaro yana cikin manyan alkawuran da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi. Mutane suna sa ran cewa zuwa lokacin da shugaba kasar zai kammala wa’adinsa, an samu saukin garkuwa da mutane tare da kawo karshen ta’addanci.

2. Tattalin arziki

Wani bangare da ake sa ran samun sauki shi ne tattalin arziki. Mutane na addu’ar ganin ranar da kaya za su yi araha, matasa zasu samu aikin yi, masu hannun jari za su narka kudinsu a Najeriya.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun tsare mutum na kwana 300 saboda ‘yi wa Buhari barazana

3. Rashin gaskiya

Duniya ta san cewa Muhammadu Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, daga cikin alkawuran da shugaban Najeriyar ya yi a 2015 shi ne za a kawo karshen marasa gaskiya.

4. Abubuwan more rayuwa

Sa-ran jama’a ne cewa nan da 2023, gwamnatin tarayya za ta kara kokarin wajen gyara hanyoyi, shimfida tituna, gina hanyoyin dogo da kuma aikin sauran abubuwan more rayuwa irinsu asibitoci, makarantu, hanyoyin ruwa da kuma wutar lantarki a Najeriya.

KU KARANTA: Trump ya yi koyi da Buhari - APC

5. Aikin gona

Komawa harkar noma ya na cikin manufofin gwamnatin shugaba Buhari. ‘Yan Najeriya suna da burin ganin abinci ya yalwata a kasar nan da 2023, tare da samun sauki a farashin kayan abincin.

A makon nan ne mu ka ji cewa wasu dalibai daga Jihohin Najeriya suna marawa Bola Tinubu baya ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Kungiyar ANSSO ta ce tana tare da tsohon gwamnan Legas kuma jigon APC, Bola Tinubu. ANSSO ta ce kishin kasar Tinubu da kuma sanin-aikinsa ta sa suke tare da shi.

Maganar takarar Tinubu ta fara nisa, har ta kai masoyansa sun zabi shugabannin yakin zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel