Ba a fara maganar shiyyar da za a kai takara a zabe mai zuwa ba inji PDP

Ba a fara maganar shiyyar da za a kai takara a zabe mai zuwa ba inji PDP

- Jam’iyyar PDP tace ba ta fara maganar yankin da za a kai takara a 2023 ba

- Umar Ibrahim Tsauri yace PDP ta na sa ran Umahi da Dogara za su bar APC

- Sanata Tsauri yake cewa akwai sauran lokaci kafin a fara batun siyasar 2023

Yayin da aka fara shiryawa zaben 2023, sakataren PDP na kasa, Umar Ibrahim Tsauri, ya bayyana halin da babbar jam’iyyar hamayyar ta ke ciki.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya nuna cewa suna sa ran gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, da tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara, za su bar APC.

Umar Ibrahim Tsauri ya fadawa jaridar Vanguard a wata hira da aka yi da shi cewa Dave Umahi, da Rt. Hon. Yakubu Dogara za su koma jam’iyyar PDP.

Sakataren na jam’iyyar PDP ya roki tsofaffin ‘yan adawar su sake sauya-sheka, su rabu da APC.

KU KARANTA: A kai takara Kudu a 2023 - Sahabi Danladi Mahuta

“Ina matukar sa ran cewa Rt. Hon. Yakubu Dogara da mai girma Dave Umahi za su dawo gidansu a 2023. APC ba wurin zamansu ba ne.” inji Tsauri.

Sanata Tsauri ya ce: “Ba za su iya zama a kungiyar siyasa (APC) ba. ‘Yan siyasa ne su, ba ‘yan kungiyar siyasa ba."

Da aka yi masa tambaya game da surutun da ake yi game da yankin da za a kai takarar shugaban kasa a 2023, sai yace ba wannan ke gabansu ba tukuna.

Ibrahim Tsauri yake cewa wasu bata-gari suna kokarin raba kan ‘yan adawa, musamman na PDP.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe dan takarar kansilan PDP

Ba a fara maganar shiyyar da za a kai takara a zabe mai zuwa ba inji PDP
Shugabannin jam'iyar PDP Hoto: Twitter Daga: @OfficialPDPNigeria
Source: Twitter

Tsauri yace babban abin da ke gaban PDP shi ne fatattakar gwamnatin jam’iyyar APC daga fadar shugaban kasa na Aso Rock a zabe mai zuwa.

“Gaskiya ne tsarin kama-kama yana cikin tsarin PDP. Amma ayi wa PDP adalci a wannan lokaci. Mun ci zabe an hana mu. Babu wanda ke maganar 2023 a yanzu.”

Kwanaki kun ji jam'iyyar APC ta jihar Kano ta yi wa jagoran PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso martani, ta ce za ta murde zaben 2023, kuma ba abin da zai faru.

Shugaban wucin gadi na jam'iyyar APC na reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas Sanusi, ya maidawa tsohon gwamnan Kano raddi na kalaman da ya yi.

Hakan na zuwa ne bayan Rabiu Kwankwaso ya sha alwashin PDP za ta karbe jihar Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel