COVID-19: Fadar shugaban kasa ta bayyana shirye-shiryen jana'izar Abba Kyari
Za a birne Marigayi Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Abuja a yau Asabar, jaridar Premium Times ta gano.
Kyari dan asalin jihar Borno ne. An sanar da rasuwarsa ne a jiya Juma’a bayan jinyar da ya kwanta sakamakon kamuwa da yayi da coronavirus.
An gano yana dauke da cutar ne a ranar 23 ga watan Maris kuma an kaishi jihar Legas don jinya.
Bayan rasuwarsa a daren Juma’a, fadar shugaban kasa ta fara shirin birne shi kamar yadda addinin Islama ya tanadar.
Jaridar Premium Times ta ji daga bakin Garba Shehu cewa za a mayar da gawar Abba Kyari Abuja daga jihar Legas a safiyar yau Asabar.
Abokan aikinsa ne za su karba gawar tashi a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja. Daga nan ne za a kammala shiri don birne shi.
Ba za a tara taro mai yawa ba don kiyaye dokokin nisantar juna saboda annobar coronavirus.
Tun bayan da aka sanar da kamuwar Kyari da muguwar cutar, ya kasance a ran jama’ar Najeriya.
DUBA WANNAN: COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki
Ya fara samun kulawar likitoci ne a Abuja kafin a mayar da shi wani asibiti mai zaman kansa a jihar Legas a ranar 29 ga watan Maris.
A wata takarda da ta fito a ranar 29 ga watan Maris, Kyari ya bayyana cewa yana samun sauki.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu sannan su kasance masu matukar tsafta don gujewa kamuwa da cutar.
A daren Juma’a ne fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa Abba Kyari ya rasu sakamakon cutar coronavirus.
A halin yanzu, Abba Kyari ne na farko a cikin manyan jami’an gwamnatin Najeriya da ya rasa ransa sakamakon annobar.
A halin yanzu, mutum 500 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya. Daga cikinsu kuwa 17 sun riga mu gidan gaskiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng