Fitattun mutanen da ake yi wa hangen mukamin COS bayan mutuwar Kyari

Fitattun mutanen da ake yi wa hangen mukamin COS bayan mutuwar Kyari

A ranar 17 ga watan Afrilu ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya watau Abba Kyari ya yi numfashin karshe a Duniya. Cutar COVID-19 ce ta kashe hadimin shugaban kasar.

Jim kadan da bizne marigayi Abba Kyari, an fara magana game da wanda zai dare wannan kujerar mai muhimmanci. Malam Kyari ya rike wannan mukami na kusan shekaru biyar.

Daily Trust ta ce akwai mutane akalla 37 da ke harin wannan kujera ta shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa. Daga cikin su akwai har gwamnoni, tsofaffin ministoci da sanatoci.

Kawo yanzu shugaba Muhammadu Buhari bai fara maganar wanda zai maye gurbin aminin na sa ba. Sai dai mun kawo wasu daga cikin wadanda ake zaton za su iya samun mukamin:

1. Ambasada Babagana Kingibe (Tsohon SGF, ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa)

2. Adamu Adamu (Ministan ilmi)

3. Kanal Hamid Ali (Shugaban hukumar kwastam)

4. Malam Nasir El-Rufai (Gwamnan jihar Kaduna)

5. Mohammed Babagana Monguno (NSA)

6. Sanata Hadi Sirika (Ministan harkokin jirgin sama)

7. Mohammed Musa Bello (Ministan birnin tarayya)

8. Kashim Shettima (Sanata kuma tsohon gwamnan Borno)

9. Kwamred Adams Oshiomhole (Shugaban APC)

10. Gwamna Mai Mala Buni (Tsohon Sakataren APC)

KU KARANTA: Manyan APC sun bada shawarar yadda za a fito da sabon COS

Fitattun mutanen da ake yi wa hangen mukamin COS bayan mutuwar Kyari
Ana tseren wanda zi gaji Marigayi Abba Kyari a Fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

11. Nuhu Ribadu (Tsohon shugaban EFCC)

12. Rotimi Amaechi (Ministan sufuri)

13. Ogbonnaya Onu (Ministan kimiyya da fasaha)

14. Janar Mohammed Buba Marwa (Tsohon gwamnan Soji)

15. Janar Abdurrahman Bello Dambazau (Tsohon Ministan cikin gida)

16. Ahmed Rufa’i Abubakar (Darektan NIA)

17. Abubakar Malami SAN (Ministan shari’a, AGF)

18. Lai Mohammed (Ministan yada labarai)

19. Faruk Adamu Aliyu (Jagoran APC)

20. Sam Nda-Isaiah (‘Dan jarida kuma jigon APC)

Ragowar wadanda aka ambata a cikin wannan jeri su ne:

21. Jalal Arabi (Tsohon sakataren din-din-din a fadar shugaban kasa)

22. Garba Shehu (Mai magana da yawun shugaban kasa)

23. Boss Mustafa (SGF)

24. Isa Ali Ibrahim Pantami (Minista)

25. Manjo Hamza Al-Mustapha (Tsohon CSO)

Kawo yanzu dai babu wanda zai iya ce maka ga wanda ake tunanin shi zai rike wannan mukami. Babu shakka Marigayi Kyari ya na cikin mashahuran hadiman da aka taba yi a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel