Jerin sunaye: Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da sabbin nade-nade
- Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da sabbin sauye sauye a tsakanin jami'anta
- Rundunar ta sauya wa wasu kwamishinonin yan sanda wuraren aiki
- Har ila yau hukumar ta nada wasu jami'ai a sabbin matsayi
Hukumar yan sandan Najeriya a ranar Laraba, 13 ga watan Janairu, ta sanar da turawa tare da sauya wa wasu jam’ai wuraren aiki zuwa hukumomin rundunar tara a kokarin yin sauyi a kasar.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a, Aremu Sikiru Adeniran ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, a shafin sadarwa na rundunar.
Aremu ya ce sauyin zai fara aiki a nan take, inda ya kara da cewa dole dukkan jami’an da aka yi wa sauyi su koma sabbin tashoshinsu.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya amince da nadin jakadu 95
Jerin sunaye da matsayinsu sun hada da:
1. Jihar Kebbi - CP Adeleke Adeyinka Bode, mni
2. SPU, FHQ, Abuja – CP Philip Maku
3. Jihar Sokoto – CP Ali Janga Aji
4. Armament, FHQ, Abuja - CP Ohikere S. Idris, fsi
5. CMDT Police College Ikeja -CP Daniel Sokari-Pedro, mni
6. Port Authority Police (PAP), Western, Lagos - CP John O. Amadi, mni
7. Jihar Oyo - CP Ngozi Onadeko, fdc
8. Jihar Enugu - Mohammed Ndatsu Aliyu
9. Border Patrol, FHQ, Abuja - CP Haladu Musa Rosamson, fdc
10. Jihar Cross River - CP Sikiru Akande
11. Jihar Ebonyi - CP Aliyu Garba
KU KARANTA KUMA: Dan kasuwa ya sayi wayoyin iPhone har na N45m amma babu komai a kwalayen
12. Hukumar filin jirgin sama - CP Abubakar Umar Bature
13. Sashin ayyuka, FHQ - CP Yusuf Ahmed
14. Jihar Adamawa - CP Aliyu Adamu Alhaji
15. Sashin horo - CP Babaita Ishola
16. Jihar Imo - CP Nasiru Mohammed
18. Jihar Delta -CP Ari Mohammed Ali
19. Sashin yaki da ta’addanci, FHQ, Abuja - CP Olofu Tony Adejoh
20. Peacekeeping, FHQ, Abuja - CP Sadiq Idris Abubakar
21. Jami’in hulda da jama’a na rundunar - CP Frank Mba.
A wani labarin, Gamayyar kungiyoyi uku na ma'aikatan jami'a sun shirya tafiya yajin aiki idan aka gaza cimma bukatun su kafin kwana uku.
Tuni sun tsunduma zanga zanga bisa rashin amincewa da ingancin tsarin IPPIS.
Shugaban kungiyar ya ce suna da yakinin gwamnati zata duba bukatar su saboda kar su kawo tsaiko a karatun yara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng